Wike da Fubara: Allah Ne Kadai Zai Iya Magance Rikicin Siyasar Jihar Ribas – Shehu Sani
- Katsina City News
- 09 Jul, 2024
- 391
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce Allah ne kadai zai iya magance rikicin siyasar jihar Ribas.
Da yake wallafawa a shafin sa na X, Sani ya rubuta: "An bar jihar Rivers a hannun Allah don magance matsalar siyasar data addabeta."
Jihar Ribas dai na fama da tashe-tashen hankula a siyasance tun bayan hawan Gwamna Sim Fubara wanda ya gaji ministan babban birnin tarayya Abuja.
Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike na fada ne kan wanda ke da iko a siyasance a jihar wanda kuma hakan ya bar baya da kura.
Rikicin ya haifar da samun masu magana guda biyu, Martin Amaewhule da Victor Oko-Jumbo.
Shiga tsakanin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a baya bai haifar da sakamakon da ake tsammani ba.
Daga: Abbas Yakubu Yaura