Ana Zargin Shugaban Kwamitin Unguwa da Kashe Matashi a Katsina

top-news

Mohammad A. Isa, Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Iyayen wani matashi mai suna Aliyu Muhammad ( Khalifa) a unguwar Kwabron Dorawa, Katsina, suna zargin shugaban kwamitin kula da unguwar, Alhaji Sabo, da kashe yaron su bayan ma'aikatansa sun yi masa duka.

A yayin wani taron manema labarai da suka kira a safiyar Lahadi, iyayen yaron da danginsa suka tabbatar da wannan zargi.

Sun bayyana cewa Alhaji Sabo ya umarci yaron ya ba da babur dinsa don kai wasu da aka kama zuwa ofishin 'yan sanda, amma yaron ya ki amincewa saboda ba shi da alaka da kwamitin. Sun ce Alhaji Sabo ya amshi babur din yaron tare da zaginsa.

Kanen mahaifin yaron, Malam Nababa, ya ce ya je ya ba Alhaji Sabo hakuri, amma daga bisani ya ji labarin cewa an kai yaron ofishin 'yan sanda bayan an yi masa duka, lamarin da ya kai ga mutuwarsa bayan an kai shi asibiti.

Mutuwar yaron ta jawo zanga-zanga daga matasan unguwar, inda jami'an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su, har wani matashi mai suna Isiya mai caji ya rasu, wasu kuma suna asibiti.

Wasu mazauna unguwar sun koka da yadda kwamitin karkashin Alhaji Sabo ke wuce gona da iri wajen ladabtar da yara, suna zargin rashin kulawar hukuma kan ayyukan kwamitin. Sun ce wannan ba shi ne karo na farko ba.

Mun yi kokarin jin ta bakin Alhaji Sabo, amma abin ya citura. Mun tuntubi hukumar 'yan sanda ta hannun jami'in hulda da jama'a, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ya ce suna kan bincike.

NNPC Advert