Mun biya sama da N275m Ga waɗanda harin jirage ya rutsa da su A kauyen Tundun Biri -Gwamnatin Kaduna
- Katsina City News
- 07 Jul, 2024
- 489
– Inji Gwamna Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa Gwamnatinsa ta raba sama da Naira Miliyan 275 daga asusun gwamnati da na sirri ga wadanda harin Tudun Biri da jirgi mara matuki ya shafa a jihar.
Gwamnan ya kuma bukaci daidaikun mutane da waɗanda suka yi alkawari lokacin da lamarin ya faru a watan Disambar 2023 da su cika alkawuran da suka dauka. Ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da shirin sake tsugunar da mutanen da rikici ya rutsa da su a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a Jiya Juma’a.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shatima ne ya kaddamar da shirin sake tsugunar da matsugunin, Sannan ya bi sahun sauran musulmin da suka yi sallar Juma’a, tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati ciki har da Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi.
A nasa jawabin, Gwamna Sani ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa zabar Tudun Biri domin kaddamar da shirin tsugunar da waɗanda rikici ya shafa.
Mun raba sama da N275,000,000 daga gudummawar daidaikun mutane da hukumomi da masu zaman kansu. Ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga duk wadanda suka yi alkawari da su ƙoƙarin cikawa kamar yadda Shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa suka yi.”
A cewar Gwamnan, a Ƙarƙashin wannan aiki da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ke gudanarwa, za a gina matsuguni guda hudu a ƙananan hukumomin Igabi, Ikara, Giwa, da Kauru ga wadanda rikicin ‘yan fashin ya rutsa da su. Aikin zai hada da gina gidaje, asibitoci, da makarantu don taimakawa waɗanda abin ya shafa su sake Rayuwarsu.