Batun LGBT a SAMOA Ba Gaskiya Ba Ne
- Katsina City News
- 06 Jul, 2024
- 473
Na Dr. Aliyu U. Tilde. 6 Yuli, 2024
Zuwa yanzu duk masu sharhi da suka yi nazarin takardun karshe game da yarjejjeniyar kasashen Turai da na Afirka, Pacific da Carribean, sun tabbatar cewa babu batun tilasta wa kasashe yin dokokin da za su halalta harkokin yanluwadi da madigo watau LGBTQ, ba kamar yadda wasu mutane da jaridu suka ce ba daga farko.
Batun LGBT
Tabbas, da farko Turawa sun nemi ayyana kyale gudanar da harkokin LGBT din a cikin daftarin farko na yarjejjeniyar, wanda ya biyo bayan taron da aka yi a Cotonou tun zamanin Buhari. Amma da aka fito da daftarin da za a sa wa hannu bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin kasashen, sai kasashen Afirka 30 suka ki sa hannu saboda gudun shigo shigo ba zurfi da ke cikin daftarin game da kare hakkokin yan LGBT.
Daga baya Turawan sun ba da kai bori ya hau inda suka aminta cewa a takaita ga aiwatar da hakkokin bil’adama da ke cikin yarjejjeniyoyin majalisar dinkin duniya, kamar na Beijing da Cairo, cewa sun wadatar. A bisa haka ne kasashen Afirka din suka aminta suka fara sa hannu kan daftarin da ya kunshi harkokin habaka kasuwanci, kyautata zamantakewa da kare hakkin dan’adam, da inganta yanayi, da sauransu.
A ganina kasashen Afirka sun taka rawar gani da suka nuna rashin yardarsu miraran da batun hakkin yan LGBT. Da ma luwadi ba dabi’ar bakar fata ba ne. Wannan zai zame shaida a gare su nan gaba.
Ka’ida
Bayan haka, ba wata jarjejjeniya da za ta yi aiki a kan kasa (legalized) sai idan kasar ta tabbatar da ita (ratifying) bisa tsarin dokokinta. Sa hannu yana nuna niyya ne kadai ba yarda ba, inji masana. Don haka wannan yarjejjeniyar badilatun ce sai majalisun dokoki na kasa sun yarda da ita. Majalisun kuma ba za su yarda da ita ba sai ta dace da dokokinmu wadanda, alhamdulillahi, dama can sun hana badalar LGBT.
Cin Mutunci
Da mamaki yanda wasu suka rika cin mutuncin jama’a da yi musu kazafi kan batun yarjejjeniyar SAMOA din ba tare da sun tantance abunda ta kunsa ba ko tabbas mutanen da suke ketawa mutunci sun yarda cewa a yi doka don halalta auren jinsi daya. Kuma wai za a ba Najeriya bashin dala biliyan 150! Kai jama’a! Ina Turawan suka ga dala biliyan 150 har da za su ba Najeriya kadai?
Na fahimci da yawan masu keta mutuncin mutane siyasa suka mai da abin don sai suna danganta shi da Muslim-Muslim Ticket. Haka suke yi a kan kowane batu da ya shafi gwamnati wanda bai musu dadi ba ko suna neman suna ko goyon baya a siyasance.
In ba haka ba, wane dare ne jemage bai gani ba a kasar nan. Mun ga sauran tiket dabam dabam (CCT, MCT, CMT) amma ba su kawar da lalacewar naira ko tsadar abinci ko rashin tsaro ko lalacewar ilimi da sauransu ba. Yau duk gazawar wadancan gwamnatocin an yafe musu sai Muslim-Muslim ticket ne damuwar. Kuma na MMT na Najeriya ne kadai illa. Sai kace MMT na Sudan, da Aljeriya, da Masar da Libiya da Iraqi da Yaman ba su da matsaloli. To sai yankasashen su nemo kirista su mulkesu ke nan.
Ba abin da ya fi ba ni mamaki kamar mutum ya sa rigar malanta amma ya rika zagin malamai yan’uwansa, yana kiransu munafukai, don kawai gwarzonsa ya fadi zabe a 2023. A maimakon ya dauka Allah ne bai ba shi ba, sai ya yi ta kumfar baki yana ashariya. Kamar malaman da yake zagi sun yarda da duk abinda gwamnati ta yi don kawai sun goyi bayanta lokacin zabe. Wannan abin babu takanoloji a cikinsa. Kai, ka ce babu hankali ma kawai. Faduwa zabe ba dadi amma bai kamata ya makantar da mutum ba.
Ya Kamata
Ya kamata, idan ana son alheri, masu fada a ji su rika magana bisa hujja—idan an kawo magana su tantance ta, sannan idan za su yi magana su yi adalci, idan kuma za su saba da wani, su guji zagi, don yin haka dabi’ar munafukai ne inji Manson Allah.
Ya kamata kuma, kamar yadda na fada a baya, gwamnati ta bugo yarjejjeniyar SAMOA gaba dayanta a shafinta na yanar gizo don fayyace wa yankasa komi. Na ji dadin yadda Ministan yada labaru ya fito fili ya ce tabbas an sa hannu. Wannan ya nuna dattijantaka saboda da ma ya yi alkawarin ba zai mana karya ba. Kuma ya yi bayani cewa ba batun LGBT a ciki. Amma duk da haka, don a yi wa tukfkar hanci, zai yi kyau idan yankasa za su ga hakikanin yarjejjeniyar gaba dayanta, ra’ayal aini. Ka ga an wuce wurin ke nan. Gaskiya tà kore karya.
Tattalin Arziki
Damuwar Turawa ba ma LGBT ba ne. A’a. Suna neman yanda za su dabaibaye mu ne ta mallake tattalin arzikinmu ganin cewa kasar Sin ta sha gabansu a yanzu kuma mu kasashe masu tasowa mun fi aminta da ita. Wannan yarjejjeniyar SAMOA wata kafa ce ta garkame mu. Ya kamata mu tsai da hankalinmu kan nazarin sassan tattalin arziki da ke cikinta wadanda za su raba mu da yancin sarrafa arzikin da Allah ya mana a maimakon mu mai dai hankalinmu kan abinda an tabbatar ba zai yu ba na LGBT.
Madalla.