Tatsuniya ta 38: Labarin Makauniya Da Danta
- Katsina City News
- 05 Jul, 2024
- 348
Gatanan gatanan ku
A wani ƙauye da ke yamma da Dajin Kurege, akwai wani manomi da matarsa makauniya. Suna zaune cikin ƙanƙanta, sai Allah ya ba su ɗa mai suna Zama. Uwarsa ta sha wahala wajen renonsa. Kullum sai ta je yin bara kafin ta ciyar da kanta da ɗanta. Mijinta bai bar musu dukiya ba sai shanu biyu kawai da Zama ya gada. Ita kuma mace mai tsinkaye da rikon amana, ta kai shanun nan wani garke a rugar wasu makiyaya da ke kusa da ƙauyensu. Ta yi haka ne da nufin idan yaron ya girma, kuma shanun sun yadu, za ta nuna masa abin da ubansa ya bar masa. Duk abin da danta yake so takan je ta samo masa.
Sannu a hankali, yaro ya girma ya isa aure. Wata rana bayan sun ci abincin dare, sai uwar ta kira shi ta ce: "To, Zama, da ma ina jira ne idan ka yi hankali sosai in danka maka abin da ka gada daga mahaifinka. Amma na kai su garke ne, a rugar wasu makiyaya."
Da ya ji lafazin mahaifiyarsa, sai ya tambaye ta: "Mene ne? Wane irin abu ne?"
Ta ce: "Shanu biyu ne ya bar maka, amma ban sani ba ko yanzu sun karu?" Sai ta kama hannunsa ta ce: "Mu je inda aka kai shanun, mu jiyo labari." Ta yi masa kwatancen hanyar da za su bi; suka kama hanya har suka kai.
Mai garke ya yi musu maraba suka gaisa kamar yadda ya kamata, sai makauniya ta tuna masa shanun da ta kawo masa kiwo tun shekarun baya. Sai mai garke ya ce: "Haka aka yi kuwa. Ai yanzu shanu sun hayayyafa, har ma sun kai ashirin."
Da ta ji haka sai ta yi masa godiya, ta ce da shi: "To, ga magajinsu ya kawo karfi, bukatu sun taso, shi ya sa muka zo mu kora su."
Sai mai garke ya ware musu shanunsu; suka kama hanyar gida, Zama yana kora su har suka je gida.
Bayan sun dan huta da kwana biyu, sai uwar ta ce da Zama: "Ya kamata yanzu kam ka yi aure domin ina so in sami jikan da zan rinka wasa da shi."
Sai ya ce da ita: "To, amma fa ni ba zan yi aure a ƙauyen nan ba sai dai daga birni."
A kwana a tashi, wata rana sai Zama ya shiga birni, ya je kasuwa, sai ya tarar an sa wata kyakkyawar yarinya a gaba, makada na cashewa ana yi mata kirari, da wake-wake. Sai ya tambayi wani dan kallo da ke wurin: "Me ya sa aka kewaye wannan yarinya mai kyau kamar aljana, ana yi mata kida da waka?"
Sai ya ce da shi: "Saboda kyaunta ne uwarta ta ce duk mai son ta, sai ya ba ta duk dukiyar da ya mallaka kafin ya aure ta. Duk masu dukiyar da ke garin nan kuma sun kasa."
Da ya ji haka sai ya yi tsaki, ya ce: "Ni zan aure ta." Sai ya matsa kusa, ya sa aka yi sanarwa, ya ce: "A gaya wa uwar yarinyar cewa ni zan aure ta, kuma zan ba da duk dukiyar da na mallaka."
Wani daga cikin danginta ya ce: “To me ka mallaka?"
Zama ya ce: "Ina da rikakkun shanu ashirin."
Sai dangin ya ce: "To, ka je ka kawo su za a ba ka ita."
Da Zama ya ji haka, sai kurum a cikin doki ya koma gida ya gaya wa mahaifiyarsa cewa ya sami wadda zai aura.
Uwar ta ce: "Wane sharadi iyayenta suka sa maka?"
Sai ya ce: "Sun ce sai na ba su duk dukiyata kafin su ba ni ita."
Uwar daga farko ta yi murna, amma da ta yi tunani kadan sai ta ce: "Kai ɗan nan, wannan fa shi ne iyakar abin da ka mallaka, babu hikima a ce ka ba su ita gaba ɗaya."
Wannan magana dai ba ta shigi yaron ba. Sai kawai ya ce shi fa sai ya auri wannan yarinyar. Sai uwar ta ce: "Shi ke nan, yi abin da kake so."
Ya kora shanu, ya kai su gidan iyayen yarinyar da zai aura. Suka karba suka kuma ba shi yarinyar, aka ɗaura aure ya dauki matarsa ya kai ta gidansu, ya je kuma ya sanar da mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: "Ai ya kamata ka kai ni in yi mata barka da zuwa."
Bai yi wata-wata ba ko sai ya kama sandarta ya kai ta har dakin amaryar. Amma da ta ga mahaifiyar Zama makauniya ce, sai ta ki yi mata magana, ta nuna cewa ai ba ta yi wa makafi magana. Uwar kuma ba ta nuna damuwa a kan halayyar surukarta ba, saboda hakurin da Allah ya ba ta.
Ana nan, bayan 'yan kwanaki sai amarya ta ce da Zama: "Ni fa na gaji, ba zan iya ci gaba da girki a gidan nan ba."
Sai ya ce: "To, yaya kike so a yi?"
Ta ce da shi: "Mai dafa abinci za ka nemo mini."
Da ya ga matarsa ta kafe a kan haka sai ya gaya wa mahaifiyarsa. Ita kuma ta ce da shi: "Ba komai, ni zan ci gaba da dafawa; ai dama tun kafin ta zo, ni nake dafawa". Haka ta ci gaba da yi musu girki, surukarta kuwa ta ci gaba da zaman ƙwambo.
Wata rana matar Zama ta tambayi mijin inda ya samo shanun da ya kai gidansu ya aure ta. Sai ya kwashe labarin yadda ya ci gadon mahaifinsa, ya gaya mata. Da ta ji haka sai ta ce: "Ai mahaifiyarka ta cuce ka domin ta boye sauran shanun. Ka je ka bincike ta da kyau, za ta gaya maka inda sauran suke."
Nan da nan ya tashi ya je ya sami mahaifiyarsa, ya fara yi mata rashin ladabi da fada, wai sai ta fito masa da sauran shanunsa. Ita kuma ta ce da shi: "Haba ɗana, ban boye maka komai ba."
Haka dai Zama ya yi ta yi wa mahaifiyarsa rashin ladabi har tsawon wasu 'yan kwanaki.
Da matar Zama ta ga bai yi wa mahaifiyarsa wulakanci kamar yadda take so ba, sai ta ce da shi: "Ni fa zan koma gidanmu; domin na gaji da zama da makauniya a gidan nan. Yanzu lallai sai ka san inda za ka kai ta, ko kuma ni in tafi gidanmu."
Sai ya ce: "Kada ki damu. Yanzu fadi yadda kike so a yi da ita."
Jin haka ya sa ta yi murmushi ta ce: "Ina son ka kai ta cikin jeji inda kuraye suke shan ruwa, sai ka ce ta jira ka, kai kuma ka gudo gida. Washe-gari sai ka je ka kwaso kasusuwanta bayan kuraye sun cinye ta. Daga nan sai ka gaya wa mutane cewa ta yi batan kai ne a jeji, kuraye suka cinye ta."
Ya ce: "Idan na yi haka za ki hakura da komawa gidanku; za ki zauna da ni?"
Sai matar ta kashe murya, ta dube shi, ta ce: “Kwarai kuwa. Idan ka yi haka, ba inda za ni."
Zama ya je ya ce da mahaifiyarsa: "Yanzu na yi wani tunani ina son ki zo mu je in kai ki inda za ki sami maganin makantarki."
Sai ta ce: "To." Nan da nan ta shirya cikin murna, suka kama hanyar daji, har suka kai tsakiyar inda kuraye kan taru, ya ajiye ta a gindin wata bishiya, ya ce da ita: "Zauna nan, ni kuma zan je neman wani itace da za a hada maganin. Idan ban dawo ba, kada ki motsa daga nan."
Ta ce da shi: "To. Na gode Zama, ka kyauta da ka kawo ni gidan masu magani."
Ko bai ma damu da godiyar da take yi masa ba, sai kawai ya kama hanya ya koma gida ya baro ta a wannan dajin. Ita kuwa ta zauna tana jiransa har dare ya yi. Idan ta ji motsi sai ta ce: "Zama ne? Ka dawo?" Sai ta ji kukan kura a bayanta, amma ba ta razana ba. Wannan dajin kuma bayan kuraye da sauran namun daji, akwai aljanu a wurin da yawa. Aljanun ne ma suka zagaye ta, suna mamakin abin da ya sa ta zo wuri mai hatsari haka. Can sai daya daga cikinsu ya rikida ya je ya ce: "Ke matar nan wane ne ya kawo ki nan?"
Sai ta ce: "Dana ne Zama ya kawo ni.
Haka dai Zama ya yi ta yi wa mahaifiyarsa rashin ladabi har tsawon wasu 'yan kwanaki.
Da matar Zama ta ga bai yi wa mahaifiyarsa wulakanci kamar yadda take so ba, sai ta ce da shi: "Ni fa zan koma gidanmu; domin na gaji da zama da makauniya a gidan nan. Yanzu lallai sai ka san inda za ka kai ta, ko kuma ni in tafi gidanmu."
Sai ya ce: "Kada ki damu. Yanzu fadi yadda kike so a yi da ita."
Jin haka fa ya sa ta yi murmushi ta ce: “Ina son ka kai ta cikin jeji inda kuraye suke shan ruwa, sai ka ce ta jira ka, kai kuma ka gudo gida. Washe-gari sai ka je ka kwaso kasusuwanta bayan kuraye sun cinye ta. Daga nan sai ka gaya wa mutane cewa ta yi batan kai ne a jeji, kuraye suka cinye ta."
Ya ce: "Idan na yi haka za ki hakura da komawa gidanku; za ki zauna da ni?"
Sai matar ta kashe murya, ta dube shi, ta ce: “Kwarai kuwa. Idan ka yi haka, ba inda za ni."
Sai Zama ya je ya ce da mahaifiyarsa: "Yanzu na yi wani tunani ina son ki zo mu je in kai ki inda za ki sami maganin makantarki."
Sai ta ce: "To." Nan da nan ta shirya a cikin murna, suka kama hanyar daji, har suka kai tsakiya inda kuraye kan taru, ya ajiye ta a gindin wata bishiya, ya ce da ita: “Zauna nan, ni kuma zan je neman wani itace da za a hada maganin. Idan ban dawo ba, kada ki motsa daga nan."
Ta ce da shi: "To. Na gode Zama, ka kyauta da ka kawo ni gidan masu magani."
Ko bai ma damu da godiyar da take yi masa ba, sai kawai ya kama hanya ya koma gida ya baro ta a wannan dajin. Ita kuwa ta zauna tana jiransa har dare ya yi. Idan ta ji motsi sai ta ce: "Zama ne? Ka dawo?" Sai ta ji kukan kura a bayanta, amma ba ta razana ba. Wannan dajin kuma bayan kuraye da sauran namun da ke dajin, akwai aljanu a wurin da yawa. Aljanun ne ma suka zagaye ta, suna mamakin abin da ya sa ta zo wuri mai hatsari haka. Can sai daya daga cikinsu ya rikida ya je ya ce: "Ke matar nan kawo ki nan?"
Sai ta ce: "Dana ne Zama ya kawo ni, don neman maganin makantar nan tawa."
Sai aljanin nan ya ce: "A'a, nan fa mutane ba sa zuwa, domin tsakar daji ne, amma zan taimake ki yadda za ki tafi gida."
Sai ta ce: "A'a, dana ya ce in jira shi a nan; idan na tafi zai yi miní fada. Gara in jira shi ai zai zo ya same ni."
Da tausayi ya kama aljanin nan, sai ya gaya mata cewa za su warkar mata da makantar. Kamar da wasa, da suka yi wani siddabaru irin nasu, sai kawai ta ga ta fara gani. Bude idonta bai sa ta yi niyyar tafiya ba, har gari ya waye ta farka daga barcin da ta yi, ta shiga jiran danta. Kafin ya zo sai ta ga shanu masu yawa, garke-garke, ta tambayi aljanin nan da ya rikida ya zama mutum, ko shanun nan na wane ne? Sai ya ce da ita, ai nata ne duka. sun ba ta kyauta.
Makauniyar nan tana zaune can sai ga Zama ya iso. Ya kuma zo ne don ya kwashe kasusuwan mahaifiyarsa saboda ya tabbatar da kuraye sun cinye ta a cikin dare. Maimakon haka, sai kawai ya ji ta kira shi daga nesa, saboda jikinta ya ba ta cewa danta ne, ko da yake dai ba ta taba ganin sa ba sai wannan rana. Har ya juya zai gudu sai ta ce: “A'a, kada ka gudu mana. Ni ce mahaifiyarka."
Da ya isa kusa da ita, sai ta kwashe duk labarin abin da ya faru tsakaninta da mutumin da ya taimake ta, ga idanu sun samu, kuma ga shanu. Zama ya kora shanu, shi da mahaifiyarsa suka koma gida. Da matarsa ta gan shi da garken shanu, kuma ga mahaifiyarsa tana gani radau, sai haushi da mamaki suka kama ta. Shi kuma Zama ya kwashe labari ya gaya mata. Jin haka ya sa ta ce ita ma dole ne ya kai uwarta dajin nan idan yana son zama da ita. Sai ya ce: "To, zan yi duk abin da kike so, saboda ina son ki."
Bayan kwana uku da dawowar uwar Zama daga dajin mutuwa, matarsa ta tafi garinsu, ta dauko uwarta, domin ita ma a kai ta can ta samo shanu. Haka kuwa aka yi ya dauke ta ya kai ta daji ya baro. Da ta ji kukan kura na farko, sai ta kidime ta kama ihu, ta tsure. Nan take kuwa kuraye suka far mata suka cinye ta.
Da gari ya waye Zama da matarsa suka kama hanyar daji domin su koro shanun uwar matarsa, amma da suka je inda suka kai ta, sai suka tarar da kasusuwanta kuma ba shanu. Tun daga dajin matar Zama ta kama ta kasa komawa gida ta tare a gindin wata bishiya tana ta kukan bakin ciki, ta na sharar kuka.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Gaskiya da rikon amana su ne maganin makirci da makirai.
- Hassada da ganin kyashi su suke sa a fada kogin da-na-sani.
- In za ka gina ramin mugunta, gina gajere.
- Tun ran gini, tun ran zane.
Tushe: Mun Ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman