Jami'in hukumar EFCC ya hallaka kansa a Birnin tarayya Abuja.
- Katsina City News
- 03 Jul, 2024
- 442
Wani jami’in hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ya kashe kansa a Abuja.
Jaridar Internet ta PRNigeria ta rawaito cewa an samu gawar jami’in a gidansa dake birnin tarayya Abuja.
Jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba, ya kasance haziki kuma kwararre a hukumar ta EFCC.
Rahotanni sun ce jami’in ya sha fama da cutar damuwa kafin rasuwar tasa.
Mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale, yace hukumar za ta binciki mutuwar jami’in tare da bada tallafi ga iyalansa.
Oyewale ya kara da cewa hukumar ta fahimci wasu lamura da ka iya zama su ne sanadiyar mutuwar tasa ciki har da kalubalen iyali.
Sannan ya ce hukumar ba za ta fitar da kowanne irin bayani ba ko bayyana sunan jami’in har sai an kammala bincike.