Jami'an 'Yansanda a Katsina Sun daƙile yunkurin satar mutane tare da Ceto 10
- Katsina City News
- 02 Jul, 2024
- 378
- Da sanyin safiyar Talata, wasu 'yan bindiga da ake zargi sun kai hari a wani gida dake bayan Comprehensive Quarters a karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina. Masu harin sun jiwa mutum daya rauni sannan suka sace mutane goma sha hudu.
Bayan samun rahoton, DPO na Dutsinma ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa wurin da abin ya faru inda suka gwabza da 'yan bindigar. 'Yan sanda sun yi nasarar hana satar mutanen tare da ceto mutane goma daga cikin wadanda aka sace. Abin takaici, wanda aka jiwa rauni ya rasu yana karbar magani a asibiti.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya tura tawagar bincike da ceto zuwa cikin dazukan dake kusa domin ceto sauran mutanen da aka sace ba tare da wata matsala ba, da kuma kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki. Za a ci gaba da sanar da jama'a ci gaban binciken da ake yi.