Tatsuniya ta 34: Labarin Yan Bakwai Da Aljana
- Katsina City News
- 01 Jul, 2024
- 430
Ga ta nan, ga ta nanku.
A can kusa da dajin aljannu wanda aka ce ya yi iyaka da bangon duniya, akwai wata mata mai 'ya'ya maza su bakwai. Ana nan, ana nan sai yaran suka girma, har dai suka isa aure. Da gyatumarsu ta ga sun isa aure, sai ta tara su ta ce: “Ya kamata a ce yanzu kun yi aure, tun da ga shi Allah ya sa duk kun girma, kowa ya mallaki hankalinsa.”
Da suka ji haka, sai babban cikinsu ya ce wa uwar: “Za mu yi aure, amma muna so a sama mana 'yan mata bakwai wadanda suke uwarsu ɗaya.” Sai babarsu ta ce: “Kash, amma ai duk garin nan babu irin 'yan matan da kuke so, sai dai ku tafi nema wani garin.” Sai suka bi maganar mahaifiyarsu, suka shirya suka kama hanya za su neman matan aure.
Bayan 'yan bakwai sun bar gari sun kama hanya, sun yi tafiya mai nisa, sai suka hadu da wata mata da 'yarta ɗaya suna noma. Da ta ga samari bakwai rigis, sai ta daga kai ta dube su ta ce: “Sannunku samari.” Su kuwa suka amsa gaisuwarta cikin ladabi. Sai ta tambaye su inda za su. Sai babbansu ya ce mata: “Za mu je neman matan aure ne.”
Da ta ji haka sai ta ce: “To ga 'yata idan za ku aura.” Tare da ban girma sai ɗaya daga cikinsu ya ce: “A'a, muna neman 'yan mata bakwai ne wadanda suke uwarsu ɗaya kamar mu.” Wannan bayani ya rufe mata baki, sai ta ce: “To, shi ke nan; ni dai 'yata ɗaya ce idan za ku karɓe ta.” Sai suka ce: “A'a, mun gode.”
To ashe wannan mata aljana ce ba su sani ba. Da suka yi nisa daga inda take, sai ta yi irin saurin aljannu ta je can gabansu a wata gonar da 'ya'ya mata biyu. Saboda suna da ladabi da girmama manya, a nan ma suka gaishe ta, ba tare da sun san ita ce ba, saboda ta sauya kama. Matar nan ta tambaye su labarinsu, suka faɗa mata tare da bayani a kan abin da suka fito nema. Sai ta nuna za ta ba su 'yan matan nan biyu idan sun amince. A nan ma dai cikin hikima suka yi mata bayanin cewa 'yan mata bakwai 'yan ciki ɗaya suke nema. Suka wuce suka bar ta a wannan gonar.
Da matar nan ta ga sun wuce, sai ta bace, ta je gaba ta ƙara sake kamanni. Ta shiga wata gonar tare da 'yan mata uku. Haka dai ta dinga yi musu har sai da suka kai biyar. Sai suka ce su fa sai sun sami 'yan matan da su ma bakwai ne kamar su. Sai aljana ta ƙara bacewa, ta rikida ta zama wata mata kyakkyawa mai 'ya'ya mata bakwai suna taya ta noma. Da samari bakwai suka zo za su wuce sai matar ta yi musu sallama. Da suka gaisa sai ta tambaye su inda za su. Kamar yadda suka saba yin bayani a baya, sai suka ce za su neman aure ne, to amma sai 'yan matan da za su aura ɗin sun kai bakwai, kuma 'yan ciki ɗaya kamar su.
Da jin haka sai ta ce wa babban cikinsu: “To tun da mun haɗu ni ma ina da 'yan mata bakwai 'yan ciki ɗaya kamar ku, in kun yarda sai in haɗa ku.” Sai baki ɗaya suka amsa mata: “Yawwa, yanzu muka sami matan da za mu aura.” Daga nan sai matar nan ta kai su gidanta, ta sa 'yan matan su kai wa samarin nan ruwa. Da suka debo ruwa suka kawo, sai kowacce ta ba wanda za ta aura; amma fa ruwan ba ruwa ne na gaske ba, duk jini ne, in ban da na ɗan'auta: shi yarinyarsa ba ta kawo masa ruwan jini ba.
Da 'yan matan suka tafi sai ɗan'autansu ya ce kada su sha ruwan da aka ba su saboda jini ne, ba ruwa ba. Da sauran suka ji haka, sai suka zubar, ya ba su nasa suka sha suka koshi. Can kuma sai 'yan matan suka shiga dafa wa bakinsu abinci. 'Yan mata shida suka debo naman mutane da uwar ta yi tanadi, suka shiga dafa wa samarinsu; amma ƙarama cikinsu ta ɗan autan, sai ta debo naman shanu ta girka wa masoyinta ɗan'auta. Da suka dafa abinci suka kawo wa mazajensu, sai da aka zo cin abinci, ɗan autansu ya ce su zubar da abincin domin da naman mutane a ciki. Da suka zubar sai ya kawo musu nasa suka ci, har suka koshi.
Da dare ya yi, sai aka nuna wa kowannensu dakinsa shi kaɗai. Amma da sun yi barci, sai surukarsu, watau aljana, ta fara wasa da wukarta domin ta riga ta yanke shawara idan dare ya yi za ta yanka su duka. Saboda ɗan'auta ya san abin da matar take son yi, sai ya zagaya ya shiga kowane ɗaki, yana cire wa mazan kayansu yana sa musu na mata. Su kuma matan yana sanya musu kayan mazan. Da ya gama, ya koma dakinsa ya shirya ya kama tona rami har zuwa garinsu. Da ya gama sai ya kwanta yana sauraron matar nan ta dinga shiga ɗaki-ɗaki tana yanka 'ya'yanta ba tare da ta sani ba.
Da ɗan'auta ya tabbatar matar ta gama yanke-yanken ta koma, sai ya fita ya tashi duk 'yan'uwansa don su gudu. Sai suka shiga ta ramin da ya tona suka tafi gida. Ita kuwa aljana da gari ya waye sai ta fara buga kofofin 'ya'yanta don su tashi, amma shiru. Da ta karairaya kofofin ta shiga dakunan, sai ta tarar ashe 'ya'yanta ne ta yanka gaba ɗaya. A nan take ta fara kuka.
Da ta ɗan huce, sai ta ce sai ta yi maganin yaran nan. Sai ta rikida ta zama godiya ta shiga garin 'yan bakwai. Da ta je daidai gidansu sai suka gan ta. Sai ɗan'auta ya ce a bar shi ya kama ta, sai babbansu ya ce: “Ai kai ne ƙarami don haka bai kamata ka kama godiyar nan ba.” Sai ya bar babbansu ya kama ta ya daure ta cikin gidansu yana kiwonta, har ta yi kiba, ta yi kyau.
Bayan wasu kwanaki sai ɗan'auta ya ce da yayansa: “Yau zan kai maka godiyarka rafi.” Sai ya ce: “To, na gode.” Sai ya kwance godiya ya kai rafi ya daure a jikin bishiya; sai ya samo wata babbar sanda ya fara jibgar godiyar nan yana waka yana cewa: “Ba godiya ba ce, aljana ce.” Ya doke ta sosai har ta rame. Da ya koma gida da godiyar sai yayansa ya ga duk jikinta jina-jina, kuma ta rame. Ganin haka sai yayan nasa ya kama shi da faɗa. Sai ɗan'auta ya ce: “To shi ke nan, muna nan da kai za ka zo ka yi da-na-sani.”
Washe-gari sai babban wan su ɗan'auta ya hau godiyar domin ya kai ta rafi shan ruwa. Amma da godiyar ta ga sun fita daga cikin gari, sai ta kama sukuwa kamar za ta tashi, ba ta tsaya ba sai a gidan aljanar da ta so yanka su. Tana isa ta zame, ya fado ƙasa, kuma ta rikida ta koma siffarta ta aljana. Sai ta dube shi ta ce: “'Yan banza, ni kuka kashe wa 'ya'ya, to duk sai na cinye ku. Tashi ka jika waccan tokar miyar don zan dafa ka da ita in an jima da daddare.”
Sai ya tashi ya jika tokar miya; sai aljana ta ce: “Zauna kusa da tokar don da ita zan dafa ka.” A can gida ba a ga yayan ɗan'auta ya dawo ba, sai ɗan'auta ya rikida ya koma ɗan maraki ya je gidan aljana. Daga shiga sai ya nufi inda ɗan'uwansa yake zaune, ya ture tokar da ke gabansa. Da babban ya ga haka sai ya ce wa aljana: “Kin ga ɗan maraki ya zo ya zubar da ruwan tokar.” Sai aljana ta ce: “To ka kora shi ka kai shi bakin gangaren can mai nisa.” Da ya kora ɗan maraki har suka yi nisa da gidan aljana, sai ga ɗan maraki ya koma ɗan'auta. Sai ya dubi yayansa ya ce: “Ai da ma na gaya maka ka yi hankali da godiyar nan.”
Ba dai tare da ɓata lokaci ba sai ya ce da yayansa su tafi gida.
Mun ciro wannan Labarin daga littafin "Taskar Tatsuniyoyi" Na Dakta Bukar Usman