'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda a Katsina
- Katsina City News
- 30 Jun, 2024
- 585
Katsina Times
A yau Lahadi, 30 ga Yuni, 2024, da misalin karfe 6:00 na safe, 'yan bindiga sun yi kwanton bauna ga 'yan sandan kwantar da tarzoma a hanyarsu ta zuwa garin Jibia daga sansaninsu da ke kauyen Zandam na karamar hukumar Jibia a jihar Katsina. A wannan harin, an kashe 'yan sanda biyar, an harbi guda daya wanda yanzu haka yana karbar magani a asibitin FMC Katsina ba tare da sanin inda yake ba.
Haka zalika, 'yan bindigar sun kwace bindigogi kirar AK 47 guda biyar mallakin 'yan sandan da aka kashe.
Katsina Times ta tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, PPRO Abubakar Sadiq, amma wayarsa bata shiga ba. Haka kuma, sakon karta kwana da aka aika masa bai samu amsa ba tukuna.