Bikin Babbar Sallah 2024: Gwamnatin Katsina Ta Bukaci Karin Bayani Daga Masarautar

top-news

Katsina Times 

A ranar 27 ga Yuni, 2024, gwamnatin jihar Katsina ta aika wa masarautar Katsina takardar neman karin bayani kan rashin halartar wasu daga cikin hakimai hawan sallah Babba na 2024. 

A takardar da Sani Rabiu Jibia, daraktan kula da harkokin gudanarwa, ya sa wa hannu, an bukaci masarautar Katsina ta bayyana dalilan da suka sa wasu daga cikin hakimai ba su halarci hawan sallar ba. Wannan umarni ya biyo bayan jawabin da gwamnan jihar Katsina ya yi a lokacin karamar sallah, inda ya bayyana cewa dole ne kowane hakimi ya tabbatar da halartar hawan sallah, sai dai in akwai lalurar tsufa ko rashin lafiya.

A takardar, da Sani Rabiu Jibia ya rubuta:

"Na sami umarnin in yi magana a kan wasikar ku ta ranar 7 ga Yuni, 2024, dangane da batun da ke sama, da kuma isar da umarnin mai girma gwamna cewa ku kawo dalilan rashin halartar wasu daga cikin hakimai a bikin hawan sallah Babba na 2024."

Kamar yadda aka rubuta a takardar, gwamnatin jihar na jiran amsa daga masarautar Katsina kan wannan batu. Wannan mataki na nuni da yadda gwamnati ke son tabbatar da cikakken hadin kai da kuma halartar dukkan hakimai a dukkanin al'amuran masarauta, musamman ma bikin hawan sallah Babba.

Tun a jawabin da gwamnan Katsina ya yi a lokacin karamar sallah, ya jaddada cewa dukkan hakimai suna da wajibcin halartar hawan sallah, sai dai in akwai lalura ta tsufa ko rashin lafiya. Wannan yana daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka don tabbatar da cikakken hadin kai da kuma martaba al'adun gargajiya.