ZAGAYE NA BIYU ZA A FARA YAKIN NEMAN ZABE DAGA GOBE LAHADI A ƘASAR IRAN,
- Katsina City News
- 29 Jun, 2024
- 486
-Bin Muhammad
2024-06-29 H.TV
A Iran, yan takara da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar zasu fara yakin neman zabe daga gobe Lahadi.
Yakin neman zaben zai kawo karshe sa’o’I 24 gabanin kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
A ranar Juma’a mai zuwa 5 ga watan Yuli ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu bayan da a kuri’ar da aka kada a ranar Juma’a ba a samu ko daya daga cikin ‘yan takara hudu da ya samu kason da ake bukata na kashi 50 cikin 100 domin lashe zaben tun zagayen farko, kamar yadda hedkwatar zaben kasar ta sanar yau Asabar.
Mohsen Eslami, kakakin hedkwatar zaben kasar ya sanar a safiyar yau da sakamakon karshe a wani taron manema labarai bayan sanar da kidaya kuri’u na karshe.
Ya ce daga cikin kuri’u miliyan 24.5 da aka kada, tsohon ministan lafiya Masoud Pezeshkian ya samu kuri’u miliyan 10,415,991 (42.45%) yayin da tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kasar Saeed Jalili dake biye masa da kuri’u Miliyan 9,473,298 (38.61%).
Sai Mohamed Baqir Qalibaf da ya zo na uku da kuri’u Miliyan 3,383,340 (13.78%) daga kasrhe sai dan takara Pourmohammadi mai kuri’u Dubu 206,397 (0.84%).
Ministan cikin gidan kasar Ahmad Vahidi ya yabawa al’ummar kasar da hukumomin zabe da suka gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.
An gudanar da zabukan cikin aminci da kwanciyar hankali, kamar yadda ya shaida wa manema labarai bayan kammala kidaya kuri’u.
Ana zaben ne shakara guda kafin lokacin da ya kamata a gudanar da shi sakamakon rasuwar shugaban kasar Mirigayi Ebrahim Ra’isi a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata tare da wasu mukarabansa ciki har da ministan harkokin waje Hussein Amir Abdolahian,