Gwamna Radda Ya Jagoranci Tattaunawa Kan Rashin Abinci Mai Gina Jiki a Arewa
- Katsina City News
- 28 Jun, 2024
- 524
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci wani taro kan matsalar rashin abinci mai gina jiki a Arewacin Najeriya, wanda ya gudana a Abuja. Taron, wanda Athena Centre for Policy and Leadership tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya suka shirya, ya bayyana cewa yara fiye da miliyan 10 suna fama da rashin abinci mai gina jiki a yankin.
Gwamna Radda, tare da sauran gwamnonin jihohin Zamfara da Neja, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa irin su Bankin Duniya da Médecins Sans Frontières (MSF), sun tattauna hanyoyin gaggawa da na dogon lokaci don magance wannan matsala. An ba da shawarwari kan karin rabon abinci da taimakon likita da kuma inganta ayyukan noma masu dorewa.
A karshe, Gwamna Radda ya yi kira da a dauki matakin gaggawa don magance wannan matsala a Arewa, yana mai bayyana cewa Jihar Katsina a shirye take ta yi hadin gwiwa da abokan ci gaba don cimma wannan buri.