Tatsuniya Ta 33: Labarin Wata Mayya Da Danta

top-news

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wata mayya a wani gari, tana zaune da mijinta, har ta sami rabo. Daga karshe ta haifi danta namiji aka sa masa suna Malgwi. Tun tana da cikinsa ubansa ya rasu, ya bar dokinsa, wanda yaron ya gada. Uwar ta kula da dokin har Malgwi ya girma, ya zama saurayi kyakkyawa.

Wata rana, wata kawar uwar Malgwi ta ziyarci gidansu. Sai ita da bakuwarta suka zauna a tsakar gida suna hira. Sai kawar ta ce da ita: "Ya kamata ki san yadda kika yi da danki tun da ya girma ya kai a cinye shi."

Sai uwar ta ce: "E, ai ina shiri, kuma a daren yau zan gama da shi, na ga ya fara shige-shige."

Ashe Malgwi yana bakin kofar daki yana jin duk abin da suke fada; sai ya fita waje ya sami wuri ya zauna, ya kama kukan zuci yana cewa ashe uwarsa mayya ce bai sani ba? Kuma kila ma ita ce ta cinye babansa, yanzu kuma za ta cinye shi. Nan dai ya yanke shawarar barin garin; sai ya je ya kwance dokin da ubansa ya mutu ya bari, ya daura masa sirdi ya hau ya kama hanya, ya bar garin.

Da uwar Malgwi ta fito daga daki ta ga an kwance doki, sai ta fita tana tambaya ko an ga wanda ya kwance doki. Sai wadanda suka gani suka gaya mata cewa danta ne ya wuce a kan dokin, ya bar garin. Sai ta koma gida ta sa rigar maitarta, ta fito bin sawun Malgwi. Duk sanda ta yi taku daya sai ta je kusa da shi, shi kuma sai ya kara zaburar doki, yana sulalewa yana cewa: "Dokin baba kai ni gari ba kusa ba."

Ita kuma uwar tana ba shi amsa tana cewa: "Ga ni nan Malgwi, ga ni nan dana."

Haka dai tana gudu duwawunanta biyu suna motsi suna waka suna cewa: "Ka tumbude ka durje, da ka fadi bakin maza." Ita kuma tana cewa: "Ga ni nan Malgwi, ga ni nan dana."

Haka ya ci gaba da sukuwa a kan dokin nan. In sun hadu da mutane sun tambaye shi abin da ya sa shi gudu haka sai ya ce: "Abin da ke bayana ba rarfin kowa, ku ba ni hanya."

Yana cikin wannan gudun ceton rai, sai wasu mutane suka sake tsai da shi, amma sai ya ki tsayawa har dai ya kai gabar wani babban gulbi: sai dokin ya tsaya. Da Malgwi ya ga dokin ya tsaya, sai ya fara waka yana cewa: "Dokin baba kai ni gari, ba kusa ba."

Da doki ya ji waka sai ya fada cikin ruwa yana ninkaya har suka haye, kuma suka shiga cikin wani kungurmin daji wanda ke cike da aljannu da manyan namun daji. A nan ne fa shi da dokin suka yi cirko-cirko, suka kasa yin gaba, balle kuma baya.

Da kurar hanya ta lafa, sai ga wasu manyan namun daji a tsugune suna kallon Malgwi da dokinsa. Sai suka tambaye shi labarin halin da yake ciki. Sai ya yi musu bayani. Da suka ji bayaninsa, sai suka ba shi izini ya sami wuri a gindin wata bishiya da ke kusa ya zauna ya huta.

Da ya dan zauna yana hutawa, sai namun dajin nan suka ce masa za su taimake shi. Ya daure dokinsa, ya yanki ciyawa ya sa a gabansa, doki kuma ya fara ci.

Can Malgwi ya fara hutawa, har da dan gyangyadin gajiya, sai ga uwarsa ta iso inda yake a guje, tana haki da waka. Sai daya daga cikin namun dajin nan ya bude bakinsa, wanda ya fi kofar gari girma. Ita kuwa idanunta sun rufe, ga shi ta doshi Malgwi gadan-gadan za ta yi masa rungumar mutuwa irin ta mayu, sai ta fada bakin babban naman dajin nan, ya hadiye ta. Bayan ya hadiye ta, sai ya sami ruwa ya sha, ya yi gyatsa kuma cikinsa ya dan daga kadan, amma fa bai koshi ba, saboda ya dade bai ci komai ba.

Sai namun dajin suka dubi Malgwi suka ce masa: Mun yi maka maganin mayyar nan. Idan ka ga dama sai ka kama hanya ka koma garinku. Da Malgwi ya ji haka, sai ya yi musu godiya; ya kwance dokinsa, ya daura masa sirdi, ya hau, ya haye ruwa, ya kama hanyar garinsu, bai tsaya ba har gida.

Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

- Makusancinka na iya zama makashinka.
- Ana zaton wuta a makera, ashe tana masaka.
- Mai rabon ganin badi, sai ya gani.

Tushe:
Mun ciro wannan labarin daga Littafin "TASKAR TATSUNIYOYI" na Dakta Bukar Usman.

NNPC Advert