Masu Gidajen Burodi Zasu Ƙara Farashin Burodi Karo na Hudu a Cikin Shekara Guda
- Katsina City News
- 27 Jun, 2024
- 533
Duba da tashin gwauron zabin kayan masarufi a Najeriya, masu gidajen burodi sun bayyana cewa zasu ƙara farashin burodi karo na hudu a cikin shekara guda. Wannan ƙarin farashin yana da nasaba da cire tallafin man fetur da aka yi a shekarar 2023, mintuna kaɗan bayan rantsar da shugaban Najeriya, Malam Bola Ahmed Tinubu, wanda ya haifar da tsadar kayan masarufi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Najeriya.
Wannan matsala ta sa kaso saba'in cikin dari na masu sana'ar burodi a fadin Najeriya suka rufe kasuwarsu, inji Alhaji Mansir, shugaban masu gidajen burodi a Najeriya, a wata hira da Katsina Times ta yi da shi watannin baya. Alhaji Mansir ya bayyana cewa, ba da son ran su suke wannan karin farashi ba, amma dole ce ta sanya su, domin duk mai sana'a idan ana son dorewa a cikinta to ya kirga uwa ya kirga riba.
Alhaji Mansir ya ce, "Mun yi iya yin mu, gwamnati ta shiga cikin lamarin ta tallafa wa masu sana'ar burodi amma abin ya ci tura. A cikin kayan haɗin burodi babu abin da bai kusa ninka kudinsa ba, amma su ba ninka farashi suke yi ba, suna ɗan ƙara kaɗan ne yadda za su fita ko yaya."
Ana sa ran dai karin farashin burodi zai fara aiki daga ranar Juma'a, 28 ga watan Yuni, bisa yanayin da masu sana'ar suka samu kansu.