Tatsuniya Ta 33: Labarin Maye Da 'Ya'yansa
- Katsina City News
- 26 Jun, 2024
- 374
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum a wani gari da ke gabas da garin nan. Yana da mace ɗaya da 'ya'ya biyu mata. Da suka isa aure Allah ya ba su masoya, aka yi musu aure aka kai kowacce dakinta.
Bayan 'yan shekaru kowacce ta haifi 'ya'ya. Ana nan, sai aka aika musu uwarsu ta rasu; sai dai su ba su san cewa ubansu maye ne ba, kuma shi ne ma ya cinye uwarsu tasha.
Shi ke nan yaran nan suka je gidan ubansu saboda zaman makoki, amma sai suka tarar uban nasu ya cinye gawar uwarsu tasha domin yunwar maita ta kama shi, kuma babu wanda zai ci sai gawar. Da ya ji muryar 'ya'yansa, sai ya kulle kansa a cikin ɗaki don kada su gani, su gane. Duk sanda suka kai masa abinci, sai ya ce su ajiye a ƙofar ɗaki. Bayan sun yi kwana biyu a gidan, sai a daren na uku ya tara su, ya fara zaro harshe yana haufiyar wuta. Sai suka gane cewa shi ya cinye babarsu, kuma yana so su ma ya cinye su. Da man sunan ɗaya Nkwa, ɗaya kuma Sektiraye.
Sai ya fara kiran su yana cewa:
"Nkwa da Sektiraye
Duk da 'ya'yanku,
Ku jira ni ina zuwa,
Zan cinye ku,
Da man ina jin yunwa."
Da suka ji haka sai suka kama 'ya'yansu suka buya, kuma suka ajiye kabewa a kan gado suka lulluɓe ta. Da dare ya yi tsaka, sai kawai ya tashi ya kama cin kabewar da ke kan gado. Da ya gane ba nama ba ne, sai haushi ya kama shi. Can kuma sai ɗaya daga cikin jikokinsa ya fara kuka a inda suka buya.
Da ya gane inda suka buya, sai ya yi kukan kura ya auka musu, amma bai cafki ko ɗaya ba. Sai 'ya'yan nasa da jikokin suka fito da gudu, suka kama hanyar dajin da ke kusa da garin, shi kuma yana bin su. Suna cikin gudu a dawan nan sai ya kama ɓarin jikinsa ya cinye, har dai ya zama saura ƙashi a jikinsa kawai. A hakan yake bin su da gudu yana cewa: "Dun kwalak, da ɗun kuci kal."
Da suka isa wani guri a cikin dajin, sai suka tarar wuta tana cin ciyawa, sai suka ƙeta ta cikin wutar a guje. Saboda yawancin wutar, har ta kama cin hanya. Da uban nasu yana da zaman ƙwarangwal ya isa wurin wutar nan, sai ya fadi cikinta, wuta kuwa ta cinye ƙasusuwansa, ya ƙone ƙurmus. 'Ya'yan nan nasa da jikokinsa sun sami tsira.
Da gari ya waye, sai wasu mata masu neman tokam miya suka tarar da tokam wannan maye a kan hanya, ba su san ta mutum ba ce. Sai ɗaya daga cikinsu ta ce su ɗebi tokam miya. Sai suka ɗiba, suka koma gida. Sai ɗaya daga cikinta ma ta ɗeba tokam za ta yi miya a ɗa ita. Bayan ta ɗora tukunya miya ɗa tokam a ciki ta kuma tafasa, sai ta ji miyarsa tana cewa: "Ki jira ni a hankali, domin wuta ta ƙona ni da yawa." Da ta ji haka ba ta ce ɗin ba, kuma ba ta daina girkinta ba, har sai da ta gama.
Da ta gama, ta zuba, ta kai wa mijinta abincinsa a akushinsa. Da ta je ajiye akushin sai ta ji an ce: "Idan za ki ajiye ni, ki ajiye ni a hankali don wuta ta ƙona ni da yawa?"
Da mijin ya ji, sai ya kira matarsa ya ce mata: "Na ji kamar miyarsa tana magana."
Sai ta dubi mijin tana murmushi ta ce: "Kai anya, ba kunnanka ne ba kuwa?"
Sai buɗe ya sa hannu zai buɗe akushi ya fara cin tuwo da miya, sai miyarsa ta ce: "Idan za ka ɗebe ni, ka ɗebe ni a hankali, don wutar ta ƙona ni sosai."
Da mijin ya ji haka, sai ya dubi matar ya ce: "To ashe ke mayya ce ban sani ba."
Sai matar ta ce: "A'a ai a cikin jeji na samo tokam miya."
Sai mijin ya ɗauki miyarsa ya ƙwara mata a kirji. Nan take kirjinta ya fitar da haƙora gatso-gatso, abin gwanin ban tsoro. Da mijin ya ga haka, sai ya kore ta, sai ta shiga daji, ta koma can da zama. Duk wanda ya je dajin da take zai tarar da ita tana yawo, tana cin fari da ƙwadi.
Tushen: Mun ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman