TAKAITACCEN BAYANI AKAN WASU DAGA CIKIN TSARIN HAWAN SALLAH NA TAWAGAR SARKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 23 Jun, 2024
- 339
1. DAWAKIN ZAGE.
Dawakin Zage guda goma Sha biyu ne (12). Suna daya daga cikin tsarin hawan Sallah na Tawagar Sarkin Katsina. Asalin dawakin Zage ya faro ne tun lokacin ana yake yake tsakanin Kasar Katsina da sauran Kasashe. To sai a ware wasu dawakai, a aje su gefe wadanda baza a hau su ba, maana ana ajesune don jiran ta kwana, Koda wani doki ya kaza ko ya mutu, to sai a duba daga cikin Dawakin Zage a dauko guda a masanya shi. Haka nan a ranar Hawan Sallah, zaa fito dasu don jiran ta kwana, idan wani doki ya gaza to daga cikin su zaa zabi wani. Zaa gansu farare an masu kwalliya a cikin Tawagar Sarkin Katsina.
2. TAGUWA.
Daga cikin Tawagar Sarkin Katsina na ranar Hawan Sallah, akwai wata Taguwa/ Rakumi Wanda ake ja, babu kowa a bisa shi. Wannan ta Samo asaline, da Taguwar da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya hawo daga Gidan Durbi na Kofae Sauri zuwa Gidan Korau watau Gidan Sarkin Katsina dake Kofar soro, lokacin da aka bashi Sarautar Katsina a shekarar 1906.
3. TAKOBI GAJERE.
Itace Sarkin Katsina yake rikewa a ranar Taron Sallah ko Durba. Asalinta itace Takobin da Sarkin Katsina Muhammadu Korau ya yanka Sarki Sanau acikin shekarar 1348. Muhammadu Korau shine Sarkin Katsina Musulmi na farko, asalinshi Yana daga cikin Kabilar Wangarawa, daga Kasar Mali, ya fara zama Yandoton Tsafe dake cikin Kasar Zamfara ta yanzu. Yazo Katsina, alokacin maguzanci ana Kokowa wajen zaben Sarki, yayi takara da Sarki Sanau Sarki na karshe daga Zuruar Durvi Takusheyi a inda ya kada Sanau ya yanka shi da Takobi Gajere. Tarihi ya nuna Korau shi yazo da wannan Takobin Katsina. Daga bangare guda na Takobin an rubuta ( Help from Allah and a Speedy victory) da larabci, sannan Kuma a bangare guda na Takobin an rubuta ( There is no hero except Allah and no Sword except Thulfakar).
4. TAKOBI BEBE.
Ita wannan Takobi itace Sarkin Katsina yake Ratayawa a kafadarshi a ranar Taron Sallah ko Durba. Asalin Takobin Sarkin Gobir Yakuba ce. An kwace ne Fagen Yaki, lokacin da Katsina taci Gobir da Yaki, a shekarar 1795. A lokacinne aka kashe Sarkin Gobir Yakuba, aka taho da Takobin shi a Katsina.
5. ZAGAGE.
Akwai Zagage masu shiga gaban Sarkin Katsina a ranar Taron Sallah ko Durba. Babban Zagi shike a gaba sauran suna bayan shi. Sarautar Zagi tana daya daga cikin Sarautun Tsaro, suna tsayawane a gaban Sarkin matsayin kariya ga Sarkin Katsina.
6. YAN LIHIDDA DA YAN SULKE.
Yan LIHIDDA suke suke sa Jajayen kaya da hular kwano suna bisa Dawakai a bayan Sarki. Yan Sulke sune suke sa rigar Sulke ta karfe Kuma suna rike masu. Su wadannan kamar matsayi Sojoji suke a Fagen Yaki koda yaushe suna Zagaye da Sarki.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.