Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 9 tare da Garkuwa da Mata fiye da Ɗari a Katsina
- Katsina City News
- 23 Jun, 2024
- 426
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Asabar, 22 ga watan Yuni, 'yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa sun kai hari a garin Maidabino, karamar hukumar Danmusa inda suka shafe fiye da awa shida suna aikata ta'addanci.
Mazauna garin sun shaida wa Katsina Times cewa harin ya fara ne tun daga ranar Juma'a, inda 'yan bindigar suka tare hanyar Dutsinma zuwa 'Yantumaki suka kona motocin 'yan kasuwa.
Da yammacin ranar Asabar, 'yan ta'addan sun sake shiga garin Maidabino inda suka kashe mutum bakwai tare da kone ƙananan yara biyu. Bugu da ƙari, sun yi garkuwa da mata fiye da dari sun shiga daji da su, tare da kona motoci tara da shagunan 'yan kasuwa.
Wani da abin ya faru da shi ya shaida wa Katsina Times cewa an kona masa mota, an kuma kona kayan abinci da shagunan takin zamani da suke sayarwa don harkokin gona.
Haka kuma, 'yan ta'addan sun kwashe kayan abinci da dabbobi, sauran ragowar kuma an kona su. Mafi yawan mazauna garin sun ce rashin abinci a halin yanzu ya yi tsanani, saboda kayan abincin da suka mallaka duk an kona su.
A halin yanzu, a garin Maidabino, babu mata sai tsiraru daga mazan garin, suma ba su cikin kwanciyar hankali, saboda koyaushe suna tunanin sake harin 'yan ta'adda.
Jihar Katsina dake arewacin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan bindiga. A makon da ya gabata an kashe fiye da mutum dari a kauyukan Dutsinma da Safana, tare da kwashe dukiyoyi.
Gwamnatocin jihohin Katsina da makwabtanta Zamfara, Sokoto, Kaduna, da Niger na fama da irin waɗannan matsaloli, kuma suna iyakar ƙoƙarinsu na shawo kan matsalar. A satin nan ake sa ran za a gudanar da wani taro da zai tattauna matsalolin tsaro da kuma hanyoyin magance su.