Gwamna Lawan Yana Shirin Sake Gina Zamfara: Sabon Filin Jirgin Sama a Gusau
- Katsina City News
- 21 Jun, 2024
- 444
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada aniyarsa ta sake gina Zamfara domin dawo da matsayin ta a matsayin dandalin kasuwanci a Arewacin Nijeriya.
A yayin bikin ƙaddamar da fara ginin tashar jirgin sama a Gusau, wanda Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ƙaddamar jiya, Gwamna Lawal ya ba da tabbacin sa na wannan shirin.
Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin wata sanarwa jiya cewa, filin jirgin saman Gusau zai zama ingantaccen wuri don hidimar jiragen ƙasar nan da na ƙasashen waje.
Kakakin ya ƙara da cewa, aikin zai haɗa da gina layin tashin jirage mai tsawon kilomita 3.4, sanya fitilu, da sauran na'urorin da ke taimaka wa jirage tashi da sauka.
Gwamna Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa tana da aniyar tabbatar da Zamfara ta shiga fagen gogayya a harkokin kasuwanci, wanda zai jawo hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar.
“Muna shirin gina tashar jirgin sama ta zamani da za ta ƙunshi wurin tantancewa, wurin duba jakunkuna, wuraren jira, da kuma wuraren jami'an kwastam da na shige da fice. Tashar za ta kuma samu sashen kula da hada-hadar jirage da na'urorin sadarwa irin na zamani,” in ji Gwamna Lawal.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wurin zai ƙunshi sashen kula da gyare-gyare, sashen kashe gobara da ceto, wurin ajiyar man jirgi, hanyoyin zuwa tashar, wuraren ajiye ababen hawa, ingantaccen ruwan sha, da wutar lantarki.
"Kamfanin 'Triacta Nigeria Limited' ne zai gudanar da aikin, bisa shawarar 'JBI Tech Consult', tare da yarjejeniyar kammala aikin cikin watanni 30," in ji Gwamna Lawal.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Zamfara ta kasance baya a harkokin ci gaba saboda rashin filin jirgin sama, duk da kasancewar ta cibiyar noma.
"Zamfara na buƙatar tashar jirgin sama domin haɓɓaka kasuwanci da inganta walwala da jin daɗin jama'a," in ji Keyamo. "Ina tabbatar wa Gwamna Dauda Lawal cewa, ina tare da kai da al'ummar Zamfara don ganin wannan mafarki ya zama gaskiya."