Tatsuniya Ta 30: Labarin Dodo Da 'Yar Sarki
- Katsina City News
- 20 Jun, 2024
- 1312
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana, matan wani Sarki sun je ɗaukar ruwa a rafi. Sun ajiye tulunansu suka tafi shan kanya. Kafin su dawo, sai Dodo ya zo, ya cika tulun ɗaya daga cikinsu, wanda take da ciki, da yashi, ya ɗan zuba ruwa daga sama.
Da suka dawo, kowacce ta ɗauki tulunta cike da ruwa, suka kama hanyar gida. Amma ita mai cikin ta kasa ɗaga nata tulun, kuma kishiyoyinta suka tafi suka bar ta a can. A kan dole ta shiga neman wanda zai ɗora mata tulun.
Tana nan tana jiran wanda zai taimake ta, sai can wani bakin Dodo ya bayyana, ya je wurinta ya ce: “Idan na ɗora miki tulun, to idan abin da kika haifa mace ce, za ta zama matata.” Sai ta yarda. Dodo ya ɗora mata, ta kama hanyar gida. Da ta isa gida sai ta ga akwai yashi a cikin tulun. A kwana a tashi, bayan 'yan watanni sai ta haifi 'ya kyakkyawa. Tana nan, tana jego, sai Dodo ya sami labari matar Sarki ta haifi 'ya mace, an sa mata suna Zubaina. Sai ya yi kokari ya san yarinyar, kuma ya rike kamanninta.
Shi ke nan, Dodo bai ce uffan ba, amma yana lura da 'yar har ta girma. Wata rana, sun tafi jeji ita da kawayenta sai suka hau bishiya suna tsinkar 'ya'yan bishiyar. Sai kawai ga Dodo ya zo yana kiran Zubaina wai ta sauko su tafi gidansa, yana cewa dama ita matarsa ce. Mamaki ya kama Zubaina da kawayenta. Sai ma Dodon ya shiga ba su labari yadda suka yi da mahaifiyarta tun tana ciki, har zuwa yanzu.
Da Zubaina da kawayenta suka ji haka, sai suka shiga rokon sa a kan ya bar su su tafi, Dodo kuma ya ki, ya ce lallai sai Zubaina ta sauka su tafi gidansa ta yi masa abinci su ci. Suna nan cikin wannan jayayya da Dodo, har rana ta fara sanyi. Daga nan sai ita da kawayen nata suka fara kuka da waka suna cewa: "Dodo, Dodo bar mu, mu je gida."
Shi kuma Dodo yana mayarwa kamar haka:
"Sauko, sauko,
Ba da ku nake ba,
Da Zubaina nake,
Ba da ku nake ba.
Da da ku nake,
Da na kai ku gidana."
Sai ta farko ta sauko. Da ta biyu ta zo sai ta ce: “Dodo, Dodo bar ni in je gida.” Sai Dodo ya ce: "Sauko, sauko, Ba da ke nake ba, Da da ke nake, Da na kai ki gidana." Haka ya dinga barin su suna sauka, sai da ya rage saura Zubaina ita kadai a kan bishiya, ga dare ya fara yi. Sai ta yi kashi a kan bishiya. Kamar da wasa ta dubi kashin ta ce ya taimake ta. Sai kashin ya ce: "To zan taimake ki, amma ki yi a hankali."
Da Dodo ya ji Zubaina tana magana da wani, sai ya yi tunanin ko ita da wata ne a sama. Shi dai ya kasa kunne. Sai Zubaina ta kashe murya ta ce: "Dodo bar ni in je gida."
Sai Dodo ya ce: “Sauko, sauko, Ba da ke nake ba, Da Zubaina nake, In da da ke nake, Da na kai ki gidana.” Shi ke nan da ma duhu ya riga ya yi, sai Zubaina ta sauko a hankali.
Bai gane ta ba. Tana sauka ta arce a guje sai gida. Shi kuwa Dodo da ya yi shiru, kuma ga shi yana jin yunwa, sai ya ce: "Ki sauko mana Zubaina in cinye ki."
Sai kashi ya ce wa Dodo: "Ina kan bishiya, in ka isa ka hawo mu kara." Haka dai suka yi ta yin ja-in-ja da kashi a gindin bishiya. Kafin Dodo ya farga har ya bushe saboda yunwa.
Kurunkus.
TUSHE: Mun ciro wannan labarin daga Littafin TASKAR TATSUNIYOYI Na Dakta Bukar Usman.