Mazauna Sabuwar Unguwa Sun Yaba Wa Hukumar Hisbah Bisa Rufe New Palace Hotel
- Katsina City News
- 18 Jun, 2024
- 526
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Mazauna Sabuwar Unguwa a birnin Katsina sun nuna jin daɗi bisa rufe masaukin baki na New Palace Hotel da Hukumar Hisbah ta yi. Sun bayyana hakan ne lokacin da suka kai wa shugaban hukumar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), ziyara a ranar Litinin da ta gabata.
Dattawan unguwar sun bayyana cewa, otal ɗin yana haifar da matsaloli kamar lalata tarbiyyar yara da kuma takurawa mazauna unguwar.
A nasa jawabin, Dr. Aminu Usman ya nuna farin cikinsa bisa wannan ziyara, yana mai cewa hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa. Ya kuma ƙarfafa su da su ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a unguwarsu.
A ranar Alhamis, 13 ga watan nan, Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta bada umarnin rufe New Palace Hotel ba tare da bata lokaci ba sakamakon zargin da ake yi na bata tarbiyyar yara mata. Hukumar ta ce ta gano yara mata biyu kanana a ɗaki ɗaya yayin wani bincike da ta yi, wanda hakan ya saba wa dokokinta.
A yayin sanarwar hukumar, ta ce ta yi taro na hadin gwiwa da manajojin otel-otel na jihar Katsina, ciki har da manajan New Palace Hotel, inda aka amince cewa babu wani otel da zai karɓi kananan yara. Duk wanda ya karya wannan yarjejeniya zai fuskanci hukunci mai tsanani, in ji sanarwar.
Hukumar ta ce, saboda rashin bin dokokinta da kuma gazawar otal ɗin na cika ƙa’idojin da aka gindaya, ta yanke shawarar rufe New Palace Hotel ba tare da bata lokaci ba.