ASALIN HAWAN BARIKI A MASARAUTAR KATSINA.

top-news

   Sarki na farko daya fara Hawan Bariki a Katsina  shine Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, Sarki na farko daga cikin Zuruar Sarakunan Sullubawa na Katsina. Alhaji Muhammadu Dikko an haifeshi a Katsina a Unguwar Kofar Sauri cikin shekarar (1865), yayi karatun addinin musulunci a nan cikin Garin Katsina.  Sunan kakan Sarkin Tafarki Dahiru, sunan Mahaifin Durbi Muhammad Gidado.

 Kamin ya zama Sarkin Katsina yayi Sarautar Danbarhim, Karshi, da Kuma Durbin Katsina, daga Sarautar Durbin ne ya zama Sarkin Katsina acikin shekarar 1906. Kadan daga cikin ci gaban da Katsina ta samu a lokacin shi shine, 1. An Gina Makarantar Katsina College a Katsina a shekarar 1922,  2. An bude Baitil na Arewacin Nigeria na farko a lokacin mulkin shi 3. Ya Gina babban Masallacin Jumaaa na Katsina Wanda akafi Sani da Masallacin Dutsi a cikin shekarar 1937 4. Ya kawo Hawan Bariki a Katsina. 

   Shi hawan Bariki kamar yadda bayani ya gabata Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne ya farayin shi a Katsina, yayi wannan Hawanne da niyyar yaje yakai gaisuwa wajen Rasdan na Turawa, domin a wancan lokacin Hedikwatar Turawa tana a Bariki watau G. R. A. Lokacin wannan ziyarar ne zaa a hadu a Bariki a tattauna Muhimman abubuwa da suka shafi harkan N. A da  sauransu. A inda Hakimmai da Dagattai zasu hadu domin suyi bayani akan ci gaban da aka samu na lardodinsu. Rasdan   na farko da aka fara kaima wannan ziyarar shine H. M Palmer. Mr. Palmer Baturen Ingila Wanda ya I Arewacin Nigeria Yana  dan shekara (27) a lokacin da yazo Katsina ya shaku da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a lokacin shi Sarki Dikkon Yana Durbin Katsina Kuma Yana Lieson officer watau Mai shiga hulda tsakanin Turawa da Sarkin Katsina. 

   Hawan Bariki yaci gaba a Katsina har bayan da Turawa suka bada yancin Kai,  har zuwa lokacin da Katsina ta samu Jaha acikin shekarar 1987, a lokacine Sarki zai hau yaje ya gaida gwamna a yi Walima sannan Kuma a tattauna Muhimman abubuwa da suka shafi gwamnati, sannan ayi addu'oi na ci gaban Katsina. Daga nan Sai Hakimmai su fara hawa daya bayan daya, sannan daga karshe Sarki ya hau. 

  Hawan Sallah da Hawan Bariki a Katsina ana kawata shine da shirinsi kyau. A Tawagar Sarki akwai Yan Sulke da Yan Lidda, Yan Tauri, Yayan Sarki, Yan Bindiga, Yan Zage, Yan Baka , Yan Amin, Yan Ishiriniya da sauransu. 

Alhaji Musa Gambo Kofar soro(17-06-2024).

NNPC Advert