'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Jibia, Sun Ceto Mata Uku da Jariri Dan Watanni Shida
- Katsina City News
- 16 Jun, 2024
- 495
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A ranar 16 ga Yuni, 2024, da misalin karfe 4:15 na safe, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta samu kiran gaggawa daga Jibia LGA cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a unguwar Kwata, inda suka sace mata uku da jariri dan watanni shida.
Da samun wannan rahoto, DPO na Jibia ya hanzarta jagorantar tawagar jami'an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka fafata da 'yan bindigan cikin wani kazamin fada, wanda ya kai ga hana satar.
A cikin wannan aikin ceto, tawagar jami'an ta samu nasarar kubutar da dukkanin mata ukun da jaririn ba tare da wani rauni ba. A halin yanzu ana ci gaba da kokarin kama 'yan bindigan da suka tsere.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya jinjinawa jarumta da saurin daukar matakin jami'an tsaron, tare da tabbatar da jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Katsina, in ji ASP Abubakar Sadiq Aliyu, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina.