Gwamnatin Kebbi Ta Kai Malamai 100 Hajji Duk da Tsananin Talauci a Jihar

top-news

A daidai lokacin da talakawan jihar Kebbi da dama ke kwana da yunwa tare da zullumi na rashin abin da za su ci, wasu ma sun haƙura da rayuwar saboda matsanancin halin da suke ciki, a wannan lokacin ne Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Nasiru Idris Kauran Gwandu ta kwashe kudin jama'a da sunan kai Malamai zuwa aikin Hajji.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kai su aikin Hajji da sunan wayar da kan Mahajjatan, Na’ibin limammin Babban masallacin Juma’a da ke Birnin Kebbi, Sheikh Kabir Umar-Wasagu, ya bayyana cewa masu Da’awa akalla 100 ne gwamnatin jihar ta aika Hajji bana domin faɗakar da Alhazan jihar kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Cikin sanarwar da Kakakin gwamnan jihar Kebbi ya fitar ranar Alhamis da ta gabata, ta bayyana cewa dalilin aika da masu da’awa haka shine don a wayar wa Alhazan jihar kai game da abubuwan da ya kamata su yi a lokacin aikin Hajji.

Sheikh Umar-Wasagu, wanda shima ya na cikin kwamitin masu da’awan, ya bayyana irin haka a taron bita da aka yi wa Alhazan jihar bayan sallar Azahar a garin Makka ranar Alhamis.

“Dalilin da ya sa muka taho da masu wa’azi har 100 shine don a samu wadanda za su rika tunatar da Alhazai a koda yaushe.

“Ko wacce mota muna so a saka akalla malami guda da zai rika yi musu wa’azi.”

Daga nan sai ya hori alhazai su nuna dattaku da kamala a lokacin da ake shiga motocin da za a kaisu Muna, yana mai cewa babu wanda za a bari a lokacin tafiya.

Sannan ya yi kira ga alhazan su yi taka tsantsan da kula da ƴan damfara, yana mai cewa wasu na nan sun zo ne su damfare ba aikin suka zo na Allah da Annabi.

NNPC Advert