Babbar Sallah: Wanban Faskari Ya Tallafawa Kungiyoyi Da Kayan Abinci Da Kuɗaɗe A Katsina
- Katsina City News
- 14 Jun, 2024
- 421
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Hamza Suleiman Faskari (Wanban Faskari), ya tallafawa kungiyoyi da dama domin gudanar da hidimomin Babbar Sallah.
Taimakon, wanda ya haɗa da masu buƙata ta musamman, 'yan gudun hijira, da 'yan jarida, an yi shi ne domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa da kayan masarufi a ƙasa gaba ɗaya.
Daga cikin abubuwan da kwamishinan ya raba sun haɗa da kayan abinci da kuɗaɗe ga al'umma domin gudanar da hidimomin Babbar Sallah cikin yanayi mai dadi da walwala.
Wasu daga cikin 'yan jarida da suka yi magana sun bayyana cewa babu shakka wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da hidimomin Sallah ba tare da wata matsala ba. Sun ƙara da cewa, Hon. Hamza Suleiman Faskari abokin 'yan jarida ne, kuma yana aiki kafaɗa da kafaɗa da su, yana taimakawa idan buƙatar hakan ta taso.
Da yake zantawa da wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi, Hon. Hamza Suleiman Faskari ya ce bada tallafin yana da alaƙa da irin kiraye-kirayen da Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa yake yi ga jami'ansa da su riƙa yin wani abu da zai taimaka wajen rage raɗaɗin da ake fama da shi a ƙasa gaba ɗaya.
Ya ƙara nuna buƙatar da ake da ita na faɗaɗa wannan tallafi zuwa waɗanda bala'in 'yan bindiga ya shafa a wasu ƙananan hukumomin Jihar Katsina da ke fama da hare-haren 'yan bindiga.
Kwamishinan ya jinjinawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, akan yadda yake tallafawa jama'a da abubuwan more rayuwa musamman marasa ƙarfi a cikin al'umma.