Insifekta ya Kashe Matashi Saboda Rashin Ba da Cin Hanci a Jihar Kebbi
- Katsina City News
- 13 Jun, 2024
- 428
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wani dan sanda mai suna Insifekta Nura Ahmad, wanda ya kashe matashi mai shekara 20, Ahmed Ibrahim, saboda ya ƙi ba da cin hanci.
Jabir Ibrahim, dan uwan marigayin, ya bayyana wa jaridar Sahara Reporters cewa an kashe Ahmed da tsakar ranar Laraba a yankin Zamare, karamar hukumar Yauri.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da kama Insifekta Nura tare da tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) don gudanar da cikakken bincike.
A cewar PPRO, “A lokacin da Sifeton ‘yan sandan ke bakin aiki a kan titin Zamare zuwa Yauri, Ahmad ya zo wucewa, inda Sifeton ya harbe shi a kirji. An garzaya da shi babban asibitin Yauri, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa."
SP Nafiu ya kara da cewa, “An kama Sifeton Nura Ahmad, aka tsare shi a SCID, Birnin Kebbi, don gudanar da bincike mai zurfi kan wannan lamarin. Rundunar tana miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokan arzikin marigayi Ahmed Ibrahim tare da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan rashin.”
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci wajen binciken wannan mummunan lamarin kuma za a fitar da sakamakonsa nan gaba kadan.