FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU NA MURNAR CIKAN NAJERIYA SHEKARU 25 A MULKIN DEMOKARADIYA
- Katsina City News
- 12 Jun, 2024
- 324
RANAR DEMOKARADIYA.12/JUNE/2024.
Ya ku `yan uwana `yan Najeriya bari mu fara da taya juna murnar sake ganin zagayowar ranar Demokaradiya a yau, ranar sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Wannan ranar ta zo dai dai da cikar kasar mu shekaru Ashirin da biyar a cikin mulkin Demokaradiya ba tare da katsewa ba.
A rana irin ta yau, shekaru talatin da daya baya, muka kaddamar da kudirin mu na zamowa al`ummar da ta yi cikakkiyar amincewa da Demokaradiya.
Ba abu ne mai sauki ba, kusan ma cike yake da had`arin gaske ta inda cikin shekaru shida da suka biyo baya sai da duk muka rikide muka zamo `yan gwagwarmayar kwatan `yancin kanmu a matsayin mu na `yan kasa kuma halittun Allah a ban kasa.
A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa har da wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar goma sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu daya da dari tara da casa`in da uku kuma ya zamo tambarin dimukradiyya, wato Cif MKO Abiola, da mai d`akinsa Hajiya Kudirat, da sauran wasu gwarazan irinsu janaral Shehu Musa `Yar Adua da Pa Afred Rewane, duka sun sadaukar da rayuwar su wajen samar wa Najeriya makoma mafi dacewa.
Mu yi jinjinar ban-girma ga mutanen da ba za a manta da su ba, irin su Cif Anthony Enahoro da Chif Abrahama Adesanya da Comando Dan Suleiman da chif Arthur Nwankwo da chif Chukwuemeka Ezeife da Admiral Ndubuisi Kanu da Chif Frank Kokori da Chif Bola Ige da chif Adekunle Ajasin da chif Ganiwu Dawodu da chif Ayo Fasanni da Chif Gani Fawehinmi da chif Olabiyi Durojaiye da Dakta Beko Ransome-Kuti da Chima Ubani da dai sauransu da suka riga mu gidan gaskiya.
Zai zama an yi tuya an mance da albasa idan aka manta da sadaukawar gwaraza irinsu Alani Akinrinade da farfesa Bolaji Akinyemi da farfesa Wole Soyinka da chif Ralph Obioha da chif Cornelius Adebayo ba, da dai sauran su, mutane ne da suka jure wa radadi da wahalhalun rayuwar `yan gudun hijira.
A yayinda gwarazan `yan gudun hijirar ke aiki daga nesa don tabbatar da diga-digin dimukradiyya, takwaroroinsu da ke gida Najeriya sun ci gaba da nuna juriya ga matsin mulkin sojoji. Cikin su akwai Olisa Agbakoba da Femi Falana da Abdul Oroh da Sanata Shehu Sani da Gwmna Uba sani da chif Olu Falae da saura jagororin tabbatar da ganin cewa an samar da demokaradiya irin su Chif Ayo Adebanjo da Chif Ayo Opadokun.
Sadaukarwa da gudunmuwar da wadannan hazikai suka bayar a wannan muhimmin fage, abu ne da ba za a ta6a iya biya ko a manta da shi ba.
Da babu gudumuwar jajirtattun `yan jaridar Najeriya da suka sadaukar da kafafen yada labaransu wajen isar da amon `yan rajin samar da dimukaradiyya ga duniya, da ba mu yi nasara a akan `yan mulkin kama-karya ba. Wannan ya sanya a yau za mu mika jinjinar mu ga kafafen yada labarai irin Jaridan Punch da Guardian da National Concord da Tribun da News Tempo da kuma Tell wadanda suka fusaknci katsalandan din gwamnatocin mulkin-danniya a aiyukansu har ta kai ga daure wasu `yan jaridunsu, ba don komai ba sai don sun nuna dagiya kan `yancin fadin-albarkacin baki ga `yan kasa da kuma tabbatar da nasarar za6en sha biyu ga watan yuni.
Sarkin yawa ya fi sarkin karfi! Duk da tarin karfin mulkin kama-karya, sannu a hankali sai da aka ci karfinsu har suka zama tarihi. A nan ne karfin ra`ayi da zabin al`umma suka nuna cewa suna sama da karfin bindigogi da tankokin yaki da ma duk wata barazanar masu karfi.
A shekarar 1999 Kasar nan ta samu kwato kanta daga hannun `yan kama-karya hakan ya sa ta zamo kasar Africa mafi yawan al`umma, daya daga cikin kasashe mafi yawan al`umma a duniya, kuma hasken kasashen bakar fata da ke kan turbar Demokaradiya.
Wannan sauyi ya zama wani juyin-juya-hali mai muhimmanci ga tarihin Dan Adam da ba za a taba mantawa da shi ba balle a ce ya zama kashin-yadawa.
A yau, bayan shekara ashirin da biyar, ga shi muna murnar dawowa wannan gwadabe na mulkinn
demokaradiya.
Bayan dogon nazari da hange, mun tabbatar da cewa Demokaradiya ba kayan aro ko bakon abu ba ce gare mu, don haka ba za mu yi sakaci da ita ko mu tsuke ta zuwa wani abu da ake yi daga lokaci zuwa lokaci ba, ko mu bar ta ta zamo zallar zabe da nsarar wata jam`iya a kan wata ba.
Duk da a wani sa`in, harkokin zabe kan yi kama da wasan kwaikwayo, sai dai ya kamata mu sani cewa zabe wani bangare ne na demokaradiya, amma ba dukkanta ba, Demokaradiya wani tsari ne rayuwa da ke nuna yadda ake da zaben ra`ayi ko makoma, don haka, kasa tana iya gudanar da zabe ba tare da tana demokaradiya ba, amma babu yadda za a yi kasa ta yi demokaradiya ba tare yin zabe ba.
Ta hanyar dimukradiyar ne muka raya al`adar gudanar da sahihin zabe a kasar nan, kuma wannan al`adar ta gudanar da zabe a bayyane ita ce ta tabbatar da cewa mun aminta da demokaradiya, kasancewar muna ganin yadda aka mika mulki daga gwamnati zuwa wata zababbiyar ta hanyar demokaradiya ya nuna cewa demokaradiya ta zame mana jini da tsoka.
Ya ku `yan uwana `yan Najeriya, sahihiyar demokaradiya wata fitila ce da take haskaka rayuwar al`ummar da ke karkashinta ta hanyar ba su damar yin `yantaccen tunani, da rayuwar da suke so,ta hanyar da suka zaɓa muddin bata saɓawa doka ba.
Wasu daga ababen da Demokaradiya ke kyama da inkari sun hada da yaudara ko tilasta wani ra`ayi ga masu mabambanta ra`ayoyi da hange, hasali ma ita demokaradiya a kullum tana maraba da banbance-banbancen ra`ayi da samun saɓanin fahimta, kasancewar Allah Ya halicci mutane daban daban, dole ne kowa akwai yadda yake fahimtar abu.
Demokaradiya ta fi amincewa da yi amfani da tattaunawa da musayar ra`ayoyi a matsayin hanyoyin warware saɓani, maimakon amfani da salon tursasawa.
A yayin da wasu gwamnatocin da ba na dimukradiyya ba ke tilasta wa al’ummar da suke jagoranta ra’ayoyi da manufofin da suka saɓa da buƙatunsu, ita demokaradiya tana dasa ruhin bauta wa talakawa ne a zukatan shuwagabanni na-gari, ba wai ta mai she su wasu gumaka ababen bautar talakawa ba.
Ya ku ƴan uwana masu kishin kasa. A shekaru ashirin da biyar da suka shuɗe, Najeriya ta tsinci kanta a tsakanin zaɓin ɗayan-biyu na ko dai ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ƴan mulkin kama-karya ko kuma ta zaɓi tafarkin da ya fi dacewa da ita. A wancan lokacin mun zaɓi matakin da ya fi dacewa, kuma ya wajaba mu ci gaba da bin wannan mataki a yanzu.
A matsayin mu na ƴan kasa, dole ne mu cigaba da tunatar da kawunan mu cewa, duk rintsi da tsananin da ke cunkushe a demokaradiya, ita din ce dai tsarin mulki ɗaya tilo da ya fi dacewa, dole ne mu san cewa a cikin mu akwai wasu ɓata-gari da ke hanƙoron ganin sun yi amfani da ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta don su samar da koma-baya ga tafarkin demokaradiyar da muka sadaukar da rayukan mu a dominta, idan ma fa ba su rusa shi baki ɗaya ba.
Wannan shine babban yaƙin da ke gabanmu a yanzu, kuma shine dalilin da ya sa muke bikin Ranar demokaradiya.
Babban makasudin bikin wanan rana bai takaita ga tuna-baya ko kyawawan abubuwan da suka kawo mu war-haka ba. Eh! Tabbas muna girmama rayuka da dukiyoyin da da aka sadaukar domin dora kasar nan a turbar da ta dace. Ni kaina zakaran-gwajin dafi ne a wannan shafin, tunda da ni aka dauki duk wata kasada ta ganin cewa Dimukradiya ta haifar da da-mai-ido a kasar nan, kuma a yau ni ne kan gaba cikin wadanda suka girbi abinda suka shuka a tsagin dimukradiyya.
A matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, a dabi`a da dokar kasa duka sun wajabta min tsare mutuncin wannan tafarki na gwamnatin dimukradiyya, kuma na lashi takobin kare `yancinku da walwalar ku a matsayin ku na `yan Najeriya. Kai! A shirye nake na taka duk wata rawar da ta dace wajen yin duk mai yiwuwa domin ganin demokaradiya ta cigaba da zama hanyar rayuwar mu.
Duk da cewa ƙalubalen suna da yawa da tsanani, hakan ba zai hana ni nuna farin cikina na zamowa jagoran kasar nan a wannan lokaci mai muhimmanci ga tarihin demukaradiyar ta ba.
Na gurfana a gabanku ne don na jaddada muku mahimmancin aikin da ke gaban mu a yanzu, hakika aikinmu bai takaita ga jure radadi ko iya tunkaran kalubale da makircin `yan mulkin-kama-karya ba. Ainihin aikin mu shine tunkarar jarabawar da ke gabanmu ta ganin ko za mu yi kasa a gwiwa mu kasa kare demokaradiya kawai don muna zaton inuwar mulkin- kama karya ta shude.
A nan, kuma a yanzu da muke tsaka da bikin demokaradiyan mu, ina kira a gare mu da mu sake zage dantse wajen ganin mun cika wani sabon buri wanda shi ma yake da matukar mahimmanci. Wannan buri shi ne cinma nasara a yakin bunkasa tattalin Arizikin Najeriya.
Na san muna fuskantar kalubalen tattalin arzikin mai tsanani.
Tattalin arzikin mu ya yi shekaru da dama yana bukatar garanbawul saboda shiga tsaka mai wuya da ya yi sakamakon an gina shi ne akan tubalin toka har ta kai ya kasa samun daidaito saboda dagaro da ya yi a kan kudaden shiga na man fetur kadai.
Mun bullo da sabbin tsare-tsare da za su gina tattalin arzikinmu a kan kwakkwaran tubali da zai kawo ci gaba mai dorewa, ba shakka, sabon tsarin ya haifar da radadi da matsi, sai dai ba mu da wani zabi da ya rage na gyara ga tattalin arzkin kasa wanda amfaninsa zai karade kowa da kowa nan gaba kadan sai ta wannan hanyar.
A yayin da muka dukufa kan gyaran tattalin arzikin kasa,ina mai jaddada muku cewa na dauki alwashin ci gaba da sauraron ra`ayoyin al`ummar Najeriya kuma ba zan taba juya musu baya ba.
Domin samun mafita mun tattauna da kungiyar kwadago da zuciya daya kuma a shirye muke da mu biya mafi karancin albashi. Kuma nan ba da dadewa ba za mu aike da sabon tsarin zuwa ga majalisar dokoki kasar nan domin su sanya hannu kan matsayar da aka cimma ta zama doka na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
A yayin da kungiyar kwadago ta yi kiran yajin aikin gama-gari, idan kun lura ba mu dauki matakan muzganawa ko kawo sabani a tsakanin kungiyoyin kwadagon kamar yadda aka saba gani a gwamnatocin `yan mulkin-mulaka`u ba, maimakon hakan sai muka zabi hanyar samin fahimtar juna. Babu wadda aka kama ko aka yi wa barazana, maimakon haka an gayyaci shuwagabannin kungiyar kwadago inda aka tattauna da su domin samun maslaha ta bai-daya.
Yin amfani da tattaunawa da hawa teburin sulhu sune tambarin demokaradiya, kuma su ne za su ciga ba da zama tsari na wajen mu`amalantar `yan kasa a a siyasar mu ta inganta tattalin arziki.
Na rungumi wannan tafarki ba tare da jin shayi ko son zuciya ba,kuma zan ci gaba da sadaukar da kai na a wannan bangaren har sai mun gina Najeriya mai iya yin adalci ga kowa.
A karshe ya kama mu sani cewa ba za mu iya isa ga nasara ta hanya mai sauki ba sai ta hanyar da ta fi dacewa.
Tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Roosevelt ya yi gaskiya a shahararriyar maganarsa mai cewa: “Tabbas akwai hanyoyi da dama na samin cigaba, amma daya ce a cikinsu mai dorewa”.
Mu tashi tsaye mu hana idanuwanmu bacci, mu cigaba da tafiya kada mu tsaya a tsakiyar hanya har sai mun shaida cikar burin mu na cigaban Najeriya.
Mun san tudun-mun-tsirar mu tsaf, kuma can za mu dosa. Mu hada ƙarfi da ƙarfe wajen ganin mun ɗora Najeriya da ƴaƴanta a jirgin tsira.
Ya Allah Ka ci gaba da yi wa najeriya albarka, Ka kare mana ita da demokaradiyar mu
Ina yi muku murnar zagoyowar ranar demokaradiya!