TATSUNIYA TA 28: Labarin Talipaku da Kurciya
- Katsina City News
- 12 Jun, 2024
- 525
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana, tsuntsuwa Talipaku da Kurciya suka zauna a bishiya guda. Lokacin saka kwanansu ya zo, sai suka hada kwansu a wuri guda. Bayan sun gama kwanciya, sai suka fitar da 'ya'yansu guda biyu. Suna nan a haka, kullum sai su fita neman abincin 'ya'yansu. Duk al'amuransu na tafiya cikin nasara.
To, ashe Talipaku ba ta jin dadi da bakin 'yarta ya yi tsawo fiye da na 'yar Kurciya, wadda ba wani abu da ya dami 'yarta, kyakkyawar gaske. Duk lokacin da za su fita neman abincin 'ya'yansu, sai a karbi renon 'yar Kurciya, amma a bar 'yar Talipaku a sama cikin sheka.
Ranar wata Talipaku ta yanke shawarar sace 'yar Kurciya ta gudu da ita. Wata rana suna wurin neman abinci, sai Talipaku ta sulale, ta je ta sace 'yar Kurciya ta gudu da ita.
Da Kurciya ta dago kai ba ta ga Talipaku ba, kuma suna daf da tafiya gida. Ta nemi kawarta har ta gaji, sai ta dawo gida ita kadai. Da ta shiga sheka, sai ta ga ba 'yarta, sai diyar Talipaku. Sai ta fita ta kama cigiya. Aka ce mata an ga Talipaku ta dauki 'yar Kurciya sun yi yamma.
Da jin haka, sai Kurciya ta koma shekarsu ta dauki 'yar Talipaku ta fito fur ta kama waka tana cewa:
"Talipaku, Talipaku,
Don bambancin 'ya'ya,
Nawa a gabanki,
Naki a bayana,
Kika dauki mai kyau,
Kika bar mummuna.
Garinmu, garinmu,
Garinmu da Sarki,
Mai yawa in kin je,
Sai idonki ya bata,
Mu je mu, mu je mu."
Haka dai ta dinga yin wannan waka, tana tafiya tana ci gaba da bincike har ta hadu da wasu manoma. Ta gaishe su, suka amsa, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku ta wuce? Sai suka ce: "E, tun dazu ta wuce."
Kurciya ta dauki 'yar Talipaku tana waka ta ci gaba da tafiya ta je wajen masu kiwo, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku? Sai suka ce: "E, ba ta dade da barin wurin nan ba."
Haka dai Kurciya ta ci gaba da tafiya tana waka, tana tambaya. Ita kuwa Talipaku tuni har ta isa garin Sarkin tsuntsaye ta tambayi hanyar gidan Sarki. Aka kai ta gidan Sarkin tsuntsaye. Sunan Sarkin Miki. Da ta je gaban Sarki, sai Sarki ya tambaye ta ko me ke tafe da ita? Sai ta ce ta zo ne ita da 'yarta a ba su wuri a garin domin ta zauna. Da Miki ya ji haka, sai ya ce: "To ai 'yar da kika zo da ita ba ta yi kama da ke ba. Ba 'yarki ba ce. Ina kika samo ta?"
Ita kuwa Kurciya tuni ta hadu da wasu mutane a jeji ta tambaye su ko sun ga Talipaku? Sai suka gaya mata cewa yanzu ta tambaye su hanyar gidan Sarkin tsuntsaye. Sai suka nuna wa Kurciya hanyar, suka ce ta yi sauri ko ta same ta a gidan Sarkin tsuntsaye. Nan take ta kama hanyar zuwa gidan Sarkin tsuntsaye. Tana zuwa gidan, sai ta tarar ana tambayar Talipaku a inda ta samo 'yar da ba ita ta haifa ba.
Sai Kurciya ta fara rera waka ta fadi a gaban Sarkin tsuntsaye ta yi gaisuwa, ta kuma yi wa Sarki bayani a kan yadda suka yi da Talipaku. Sai Sarki ya sa aka kwace 'yar Kurciya, aka ba ta 'yarta. Ita ma Talipaku aka ba ta 'yarta.
Sarkin tsuntsaye ya ja kunnen Talipaku da kada ta kuskura ta sake satar 'yar wani tsuntsu. Idan kuma aka sake kawo kararta, to za a kashe ta. Sai aka sallame su. Kurciya ta dauki 'yarta. Ta yi godiya ta tafi. Ita kuma Talipaku ta tafi da 'yarta.
Kurunkus.
TUSHE:
Mun ciro wannan labarin daga Littafin TASKAR Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman.