Gwamnatin Jihar Katsina Ta Yi Allah Wadai da Harin Kankara, Ta Yi Alƙawarin Ƙarawa Matakan Tsaro
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 490
Maryam Jamilu Gambo Saulawa, Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana matuƙar baƙin cikinta bisa harin da aka kai wa fararen hula a ƙauyen Gidan Boka, a yankin ƙaramar hukumar Kankara. Wannan ta'addanci mara ma'ana ya yi sanadin rasa rayukan mutane 26, ciki har da jaruman 'yan sandan mu. Gwamnati ta mika ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya haɗa kai da dukkan al'ummar jihar wajen yin addu'ar neman gafara ga waɗanda suka rasu da kuma ta'aziyya ga iyalan mamatan a wannan mawuyacin lokaci. Wannan hari ya kawo cikas ga ƙoƙarin da ake na tabbatar da tsaron dukkan al'ummar Katsina.
Gwamna Radda ya yaba da ƙoƙarin ƙwazon jami'an tsaro da ke ci gaba da yaƙi da waɗannan 'yan ta'adda da ke barazana ga zaman lafiya a jihar.
Gwamnatin Radda ta sha alwashin kawo ƙarshen 'yan fashi da dukkan nau'o'in laifuka a cikin Jihar Katsina. Gwamnati tana aiki tare da Gwamnatin Tarayya da dukkan hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki don aiwatar da tsare-tsaren tsaro don kawo ƙarshen wannan fitina.
Gwamna Radda ya yi alƙawarin ƙara yawan jami'an tsaro a Kankara da sauran yankuna masu haɗari. Ya kuma jaddada inganta ƙarfin tattara bayanan sirri don gano da kawo ƙarshen ayyukan 'yan ta'adda a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana muhimmancin haɗin kai ga al'ummomi, yana mai da hankali kan buƙatar aiki tare da shugabannin al'umma don ƙarfafa amana da samar da yanayin musayar bayanai.
Gwamna Radda ya nuna damuwa kan tushen matsalar rashin tsaro, wanda ya ce sau da yawa yana da nasaba da talauci da rashin aikin yi. Ya tabbatar da ci gaba da saka hannun jari a shirye-shiryen cigaba da ke samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa al'umma.
Ya bayyana tabbacin cewa ta hanyar waɗannan haɗin gwiwa, jihar za ta kawo ƙarshen tashin hankali da samar da zaman lafiya mai dorewa ga al'ummar Jihar Katsina.
Gwamna Radda ya yi kira ga duk wanda ke da wani bayani game da waɗanda suka aikata wannan hari da su sanar da hukumomi. Gwamnati za ta yi aiki tuƙuru don ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
"Yanzu lokaci ne na haɗin kai da ƙwazo. Muna kira ga dukkan mazauna Katsina da su kasance cikin nutsuwa da kuma haɗa kai da jami'an tsaro. Tare za mu ci nasara kan waɗannan ƙungiyoyin duhu da gina makoma mai inganci ga jiharmu," inji Gwamna Radda.