Shugaba Tinubu Ya Yi Allah Wadai da Hare-haren 'Yanbindiga a Katsina, Ya Sha Alwashin daukar mataki
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 335
Maryam Jamilu Gambo Saulawa, Katsina Times
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kakkausan suka game da hare-haren da aka kai wa jama'a a kananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina. Yayin da yake bayyana hare-haren na baya-bayan nan a matsayin "mummuna da makirci," Shugaban ya jaddada kudirin gwamnatin sa na kara inganta matakan tsaro da kuma kakkabe 'yan ta'adda da sauran masu haddasa fitina a fadin kasar.
A matsayin martani ga wadannan munanan abubuwan, Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su bi sawun maharan tare da tabbatar da an hukunta su yadda ya kamata. Ya jaddada gaggawar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasa.
Shugaban ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu, gwamnatin, da kuma jama'ar jihar Katsina. Haka kuma, ya yi addu'ar Allah Ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren.