NOMA DA KIWO: Noman Awaki: Hanyoyin da Tasirin Tattalin Arziki a Najeriya
- Katsina City News
- 10 Jun, 2024
- 367
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hanyoyin Noman Awaki a Najeriya
Noman awaki a Najeriya tsohuwar sana'a ce ta gargajiya wadda aka inganta a 'yan shekarun nan. Ga hanyoyin da aka fi amfani da su:
1. Extensive System:
- Kiwo a Fagen Daji: Ana barin awaki su yawo a fagen daji don cin ganyayyaki. Wannan hanyar na bukatar manyan filaye.
- Seasonal Migration: A wasu yankuna, ana motsa awaki zuwa wuraren kiwo daban-daban dangane da yanayi.
2. Semi-intensive System:
- Haɗakar Kiwo da Ciyarwa a Ruga: Ana barin awaki su kiwo na ɗan lokaci sannan a basu ciyarwa a ruga.
- Amfani da Filayen Kiwo na Musamman: Manoma na shuka kayan kiwo na musamman don tabbatar da isasshen abinci mai inganci ga awaki.
3. Intensive System Complete Stall:
- Ciyarwa a Ruga Kawai: Ana ajiye awaki a wurare na musamman kuma a basu ciyarwa mai cike da gina jiki daga kayan kiwo, hatsi da sinadaran abinci.
- Morden Housing: Amfani da rugage masu kyau da iska mai kyau don kare awaki daga yanayin rashin lafiya da kuma dabbobin farauta.
4. Breeding Program:
- Selective Breeding: Amfani da nau'ikan awaki na musamman don inganta samar da nama, madara da kuma haifuwa.
- Artificial Insemination: Don tabbatar da isar da ingantattun kwayoyin halitta ga zuriyar.
5. Healthcare and Management: Kulawa da Lafiya:
- Regular Vaccination- Rigakafi na Kullum: Don hana cututtuka kamar PPR (Peste des Petits Ruminants).
- Kulawar Dabbobi: Duba lafiyar awaki akai-akai da kuma magani ga marasa lafiya.
- Veterinary Care-Ciyarwa Mai Kyau: Ciyarwa mai cike da gina jiki don tabbatar da lafiyar awaki da kuma ingantaccen girma.
Tasirin Tattalin Arzikin Noman Awaki
Noman awaki yana da matukar tasiri mai kyau ga tattalin arzikin Najeriya:
1. Ƙirƙirar Ayyukan Yi:
- Ayyukan Kai Tsaye: Manoma, makiyaya, da ma'aikatan gonakin awaki.
- Ayyukan Kai Tsaye: Ayyuka a harkar samar da abinci, kula da dabbobi, sufuri da kuma kasuwanci.
2. Samar da Kuɗaɗe:
- Sayar da Awaki: Nama (chevon) yana da matukar daraja, kuma akwai kasuwa mai kyau a gare shi.
- Samar da Madara: Madarar awaki na samar da kuɗi, ana amfani da ita kai tsaye ko kuma wajen samar da cuku da sauran kayan madara.
- By-products: Fata da taki suna da daraja. Ana amfani da fatar awaki a masana'antar fata, yayin da ana amfani da takin a matsayin taki na gargajiya.
3. Tsaron Abinci:
- Tushen Furotin: Nama da madarar awaki suna samar da mahimman sinadaran gina jiki ga abincin.
- Noman Dorewa: Awaki dabbobi ne masu juriya wadanda za su iya rayuwa a yanayi daban-daban, wanda ya sa su zama tushen abinci mai dorewa.
4. Rarraba Tattalin Arziki:
- Rarraba Noma: Noman awaki yana ƙara bambanci ga harkar noma, yana rage dogaro da kayan gona kaɗai.
- Ci gaban Ƙauyuka: Yana samar da hanyoyin rayuwa da ayyukan tattalin arziki a yankunan ƙauyuka, yana taimakawa rage hijirar mazauna ƙauye zuwa birni.
5. Yiwuwar Fitarwa:
- Kasuwannin Duniya: Tare da ingantattun hanyoyi, Najeriya na iya fitar da kayayyakin awaki zuwa sauran ƙasashe, ta hanyar samun kuɗin waje.
- Kasuwancin Yanki: Ƙarfafa dangantakar kasuwanci da ƙasashen makwabta ta hanyar kasuwancin dabbobi.
6. Ƙarfafa Mata da Matasa:
- Noman Ƙananan Ma'aikata: Noman awaki yana da sauƙi ga mata da matasa, yana basu damar shiga harkar noma da inganta matsayin tattalin arzikinsu.
A taƙaice, noman awaki muhimmin aikin noma ne a Najeriya, wanda ke bayar da gudunmawa wajen samar da ayyukan yi, samar da kuɗaɗe, tsaro, Abinci, da kuma haɓaka tattalin arziki gaba ɗaya. Ta hanyar amfani da ingantattun hanyoyin noman zamani da kulawa da dabbobi, noman awaki zai iya haɓaka tattalin arzikin ƙasa sosai.
Mu jaraba Noman awaki domin samar da Ayyukan yi da habaka tattalin arziki. Zamu iya yi ko a cikin gidajen mu na birane duba da halin rashin tsaro da ya hana kiwo a dazuka da sauran garuruwa.