TATSUNIYA TA 27: Labarin Gizo Da Damon Sarki

top-news

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana Sarki ya kawo Damo babba. Sai ya kai shi gonarsa bayan gari. Bayan 'yan kwanaki kadan ya sake kawo wasu don kiwo, kuma ya sa aka yi shela a gari cewa kada a taba su, tare da bayanin cewa duk wanda ya yanka ya ci zai mutu.

Ana nan, sai wata rana kwadayin nama ya kama Gizo, sai ya zagaya inda Damon Sarki suke. Ba tare da jin wani tsoro ba ya kama daya ya yanka, ya kawo wa matarsa ta dafa masa ya cinye. Da ya ji dadi sai kullum ya zagaya ya kama daya ya yanke, har sai da ya gama Damon Sarki duka shi kadai.

Da ya karasa cinye naman Damo sarai, rannan sai ciwo ya kwantar da shi. Sai ya aika wa Koki domin ta zo ta kai shi wurin magani.

Da Koki ta dauki Gizo suka kama hanya za su neman magani, suna cikin tafiya sai suka hadu da Kura a cikin jeji. Sai Kura ta ce: "Ke Koki ina za ki?" Sai ta ce: "Zan kai Gizo ne gidan magani." Sai Kura ta ce: "In kin je ki gaya masa ba zai yi rai ba don ya ci Damon Sarki."

Sai Koki ta ce: "Wai, wai ashe cutar ba ta warkewa ba ce. Gwanin zafi, gwanin zaki."

Haka dai suka ci gaba da tafiya. Can kuma sai suka hadu da Zaki. Sai Zaki ya dubi Koki ya ce: "Ke Koki ina za ki?" Sai ta ce: "Mai girma Zaki, zan kai Gizo ne gidan magani."

Sai Zaki ya ce: "In kun je ku gaya masa Gizo ba zai yi rai ba."

Sai Koki ta yi salati, ta ce: "Ashe cutar ta fitar rai ce. Gwanin zafi, gwanin zaki."

A nan ne fa Koki ta sauke Gizo daga bayanta, ta yar da shi ta ce: "Tun da ka ci Damon Sarki, ka ci mutuwarka. Bari in bar ka a nan idan ka mutu kada ka yi musu wari a gari."

Sai Koki ta koma gida, ta bar Gizo a cikin ciwon ajali.

Kurunkus.

Mun ciro wannan labarin daga Littafin TASKAR TATSUNIYOYI Na Dakta Bukar Usman.