Gwamnan Zamfara Ya Nemi Tallafin TETFund Domin Kammala Ayyukan Gina Makarantu
- Katsina City News
- 10 Jun, 2024
- 294
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya roƙi ƙarin tallafi daga Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na TETFund domin kammala wasu gine-gine a manyan makarantun jihar.
Gwamnan ya yi wannan roƙo ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai hedikwatar Hukumar TETFund a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa Gwamna Lawal ya nemi tallafi musamman ga Jami’ar Jihar Zamfara da Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau.
Ya ƙara da cewa, Jami’ar Jihar Zamfara da ke Ƙaramar Hukumar Talatan Mafara tana da ayyuka da dama waɗanda gwamnatocin baya suka fara amma suka yi watsi da su.
“Lokacin da na ziyarci TETFund, na ambaci cewa a kullum neman ƙarin tallafi mu ke yi. A yau, na zo ne don neman ƙarin tallafi ga wasu manyan makarantun Zamfara.
“Na ziyarci Karamar Hukumar Talata Mafara makonni biyu da suka wuce na ga ayyukan da TETFund ta gudanar a Jami’ar Jihar Zamfara. Abin takaici, akwai ayyuka da yawa da aka yi watsi da su a zamanin gwamnatocin baya.
“Muna fuskantar matsaloli game da gyaran Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau, kuma ina buƙatar goyon bayan ku don warware wannan matsala.
“Zamfara na fama da ƙalubale daban-daban baya ga matsalar rashin tsaro. Lokacin da muka karɓi mulki a shekarar da ta gabata, ba a biya ma’aikata albashi ba na tsawon watanni uku, kuma ɗalibanmu ba su iya biyan kuɗin jarrabawar WAEC da NECO. Har ila yau, muna da ɗalibai da yawa a kan tallafin karatu a ƙasashen Cyprus, Indiya, da Sudan waɗanda ba a kula da su ba, da sauran batutuwan gaggawa.
“Gwamnatina ta warware matsalar albashin ma’aikata, ta biya bashin da ake bi na WAEC da NECO, sannan ta sasanta tare da daidaita biyan ɗaliban da za su samu tallafin karatu a ƙasashen waje. Mun zo nan ne domin neman taimakon ku, wanda zai taimaka sosai a ƙoƙarinmu na ceto da sake gina Zamfara.”
Da yake mayar da martani, Sakataren Zartarwa na Asusun, Arc Sonny T. Echono, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa nasarorin da ya samu a shekarar farko da ya yi kan mulki.
“Ina so in taya ka murnar cika shekara guda a kan karagar mulki, kuma ina so in yaba maka kan ayyukan da ka ke yi a ma’aikatun gwamnati, cibiyoyi, asibitoci, da sauran fannoni.
"Za mu sake duba buƙatar gwamna, kuma mu yi duk mai yiwuwa. Yunƙurin da ka ke yi wajen magance al'amuran jihar abin yaba wa ne kuma ya nuna babban matsayi. Ni kaina ina so in gode maka kan daidaita bashin WAEC da NECO," in ji Echono.