EFCC Ta Ce Za Ta Yi Aiki Akan Elrufa'i Bisa Zargisa Na Ɓanatar Da Kuɗi A Kaduna.
- Katsina City News
- 10 Jun, 2024
- 318
“Hukumar Yaki dayiwa Tattalin Arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da kuma Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa da sauran Laifuka Masu Zaman Kanta (ICPC) sun bayyana cewa har yanzu Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ba ta kai rahoto a hukumance kan zargin almundahanar Naira biliyan 423 da aka ce an tafka a zamanin tsohon Gwamna Nasiru Gwamnatin El-Rufai.
“A watan Afrilu ne Majalisar Kaduna ta kafa wani kwamiti mai mutane 13 karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Henry Danjuma, domin binciken zargin karkatar da kuɗaɗen jihar da aka yi a zamanin El-Rufa'i. an dai dorawa wannan kwamiti aikin binciken duk wasu ayyukan kuɗi, lamuni, da kwangilolin da tsohon gwamnan ya bayar, binciken ya biyo bayan kalaman da gwamna mai ci Uba Sani ya yi, wanda a yayin wani taron majalisar dattijai, ya nuna damuwarsa kan ɗimbin basussukan da gwamnatin baya na El-Rufai ta bari.
Gwamna mai ci Mal. Uba Sani yayi cikakken bayani kan nauyin da ya gada na kuɗi, inda ya bayar da misali da bashin dala miliyan 587, Naira biliyan 85, da na kwangila 115, da yake gabatar da sakamakon kwamitin, Ɗanjuma ya bayyana cewa ba a yi amfani da lamuni da yawa da aka samu a ƙarƙashin El-Rufa'i ba kuma ana yin watsi da hanyoyin da suka dace.
Kakakin majalisar Yusuf Limanne ya samu rahoton, inda ya bayyana cewa gwamnatin El-Rufa'i ta salwantar da naira biliyan 423, wanda hakan ya sa jihar ke fama da dimbin bashin kudi, wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa El-Rufai a matsayinsa na babban jami’in gwamnatin jihar daga watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023, ya karya rantsuwarsa ta hanyar cin basussukan da ba su dace ba ba tare da bin ƙa’ida ba, Majalisar ta buƙaci Gwamna Sani da ya mikia El-Rufa'i da mukarrabansa ga hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da bincike.”
Da yake mayar da martani cikin gaggawa, mai taimakawa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, yayi watsi da rahoton a matsayin maras tushe kuma abin kunya, yana mai tabbatar da gaskiyar tsohuwar gwamnatin tare da yin alƙawarin mayar da martani mai karfi da samun rahoton, a wata hira da kakakin ICPC, Demola Bakare, ya tabbatar da cewa hukumar ba ta samu wani koke daga Majalisar ba amma za ta yi bincike idan aka gabatar da irin wannan rahoto kan zargin na Elrufa'i
“Hakazalika, wasu majiyoyin EFCC da ba a bayyana sunansu ba sun bayyana cewa hukumar ma ba ta samu wani koke ba amma za ta yi aiki yadda ya kamata idan an gabatar da ita.”
Liberty TVR