Gwamnatin Jihar Katsina Ta Samu Ci Gaba a Tara Kuɗaɗen Shiga
- Katsina City News
- 09 Jun, 2024
- 449
Maryama Jamilu Gambo Saulawa, Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Jiha (KT-IRS), ta samar da kuɗaɗen haraji na sama da Naira biliyan huɗu da miliyan dari takwas a cikin watanni uku na farkon shekarar 2024.
Wannan ya nuna ƙarin kashi 227 idan aka kwatanta da abin da aka samu na sama da Naira biliyan ɗaya da miliyan dari bakwai a watanni uku na farkon shekarar 2023. Wannan nasara ta tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, za ta iya samar da kuɗaɗen shiga na cikin gida da ya haura Naira biliyan ashirin a wannan shekarar.
Wannan ya ninka kuɗaɗen shiga da jihar ta samu a shekarun baya, wanda aka samar da Naira biliyan goma ko Naira biliyan sha huɗu a kowacce shekara. Wannan gagarumin cigaba ba zai rasa nasaba da aiki da rahoton da Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kafa ba, bayan an bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina a zaɓen shekarar 2023.
Haka kuma, kowa ya san cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta samar da asusun bai ɗaya wanda ake kira TSA. Ba a fi watanni da fara amfani da shi ba, amma fara amfani da wannan tsari ya toshe hanyoyin zirarewar kuɗi da kuma bin diddigi domin kare dukiyar al’ummar Jihar Katsina.
Wannan ya nuna ƙokarin Gwamna Raɗɗa, na ganin cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta dogara da kuɗaɗen shigar da take samu na cikin gida wajen yin kasafin kuɗi nan da shekarar 2027.