TATSUNIYA TA 25: LABARIN 'YAR SARKIN DA TA SACI DINYA
- Katsina City News
- 08 Jun, 2024
- 403
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Sarki yana da 'ya'ya maza da mata da yawa. Wata rana an kawo masa dinya sai ya ajiye ta a dakinsa. Rannan sai tafiya ta kama shi. Sai daya daga cikin 'ya'yansa ta dauki dinyar ta cinye.
Da Sarki ya dawo sai ya tarar an cinye masa dinya. Sai ya tara matansa da 'ya'yansa ya tambaye su ko waye ya cinye masa dinya. Sai suka shiga yi masa rantsuwa cewa ba su suka dauka ba. Bayan an yi, an yi babu wanda ya amsa cewa shi ne ya dauka, sai Sarki ya ce da fadawansa su tara matan da 'ya'yan a kai su Kogin Rantsuwa su rantse, kuma duk wanda ya dauka to ruwa ya cinye shi, ya tafi da shi.
Suka yarda aka kama hanyar kogi. Da aka isa sai aka fara rantsuwar da matan Sarki. Duk wadda ta shiga cikin ruwan sai ta fara waka tana cewa:
"Kogi, kogi,
In ni ce na ci dinyar Sarki,
Ka tafi da ni,
Kada ka dawo da ni."
Matar farko ta fita ruwa bai tafi da ita ba. Ta biyu ma ta shiga ruwan bai tafi da ita ba, har matar karshe ta shiga ita ma ruwa bai tafi da ita ba. Daga nan sai aka shiga kan 'ya'yan Sarki maza. Aka zuba su gaba daya suka rantse, su ma ruwa bai cinye ko daya daga cikinsu ba.
Shi ke nan aka zo kan 'yan matan. Su ma aka shigar da su, ba wadda ruwa ya ci har aka zo kan ta karshe wadda ta cinye dinyar. Sai ta shiga ta fara waka tana cewa:
"Kogi, kogi,
Idan ni ce na ci dinyar baba,
Ka tafi da ni,
Kuma ka dawo da ni,
Kada ka hadiye ni."
Sai Kogin Rantsuwa ya tafi da ita. Sai matan Sarki da sauran 'ya'yansa suka juya, suka koma gida, aka je aka gaya wa Sarki abin da ya faru. Ashe duk jama'ar gidan Sarki ba su san cewa wannan yarinya da ruwa ya tafi da ita Sarki na matukar son ta ba. Dalili kuwa ita ce 'yar autarsa, sai ya yi ta kuka.
Ruwa kuwa da ya tafi da ita sai ya kai ta wani bakin jeji. Tana nan a rude, can sai ta ga wata tsohuwa tana kama kwadi. Da tsohuwa ta kyallara ido ta ga yarinya, sai ta dauke ta, ta kai ta gidanta. Yarinya ta shari barcin gajiya. Da ta farka sai tsohuwa ta tambaye ta labarin abin daya faru. Sai ta kwashe labari ta gaya wa tsohuwa. Da tsohuwa ta ji labari sai ta ce wa yarinya: "Zan taimake ki, in sauya miki kamanni. Amma da sharadi, idan kin sami mijin aure zai kawo mini buhunan tsutsa biyu."
Yar Sarki ta yarda. Nan take tsohuwa ta hadiye ta sau bakwai. Da ta yi amanta a hadiya ta bakwai sai ga yarinya ta sauya kamanni baki daya, ta zama fara jawur kamar 'yar Sarkin aljanu.
Bayan wasu shekaru, wata rana sai yarinya ta je cin kasuwa, sai ta hadu da wani dan Sarki. Shi kuwa dan'uwanta ne na jini, to amma ba ta sani ba, don sun girma ba za ta gane shi ba. Shi kuma da ma ba zai gane ta ba saboda tsohuwa ta sauya mata kamanni. Shi ke nan sai dan Sarki ya ce zai aure ta. Sai ta ce sai dai ya je wurin kakarta su yi magana. Sai ya amince, suka je wurin tsohuwa. Da tsohuwa ta ji bayanin dan Sarki sai ta ce ya je ya kawo mata buhunan tsutsa biyu. Dan Sarki ya tashi cikin mamaki. Ya je ya nemo buhunan tsutsa biyu, ya kawo wa tsohuwa. Daga nan sai aka daura masu aure. Ya dauki matarsa ya kai ta garinsu.
Bayan ya kai ta gidansu, sai ta ga ashe gidan babanta ne. Sai kawai ta shiga cikin gida gayar da surukanta. Sai ta ga ai wadda ta haife ta ce surukarta. Shi kuma mijin yayanta ne, ubansu daya. Da ta gane sai hankalinta ya tashi, amma babu yadda za ta bayyana wannan al'amari a gamsu tun da tsohuwa ta sauya mata kamanni.
Kullum idan za ta yi daka sai ta fitar da turmi a tsakar gida tana daka tana waka tana cewa:
"Babana da ya haife ni ya zama surukina,
Innata da ta haife ni ta zama surukata
Yayana da nake binsa ya zama mijin aurena,
Kannena da suke bi na sun zama abokan wasana,
Zan daki turmin gidanmu,
Zan daki turmin gidanmu timkwalan-kwalan."
Ana cikin haka kullum, sai wata tsohuwa ta kasa kunne ta ji abin da amarya take cewa. Rannan dai sai tsohuwar nan ta kira yaron ta gaya masa idan ya fita kamar za shi zaman fadanci, to ya labe a cikin gida ya saurari wakar da matarsa take yi idan tana daka, ya ji abin da take cewa.
Rannan sai dan Sarki ya fita, kamar ya tafi, sai ya labe. Jim kadan da amarya ta fara daka sai ta kama wakar tana maimaita abin da take cewa kullum. Da ya ji wakar matarsa sai ya fahimci abin da take fada, kuma ya gane cewa kanwarsa ce.
Sai ya ruga da gudu, ya kama ta, yana kuka ya ce: "Ashe ke ce 'yar autar baba, amma kika ki fada?" Ya dauke ta sai wurin babansa. Da ya yi gaisuwa, ita ma ta gai da Sarki, ya ce ta ba mahaifinta labarin abin da ya faru. Sai ta kwashe labari yadda ta cinye dinyar babanta, har ruwa ya tafi da ita. Ta fada yadda tsohuwa ta dauke ta, da yadda ta hadiye ta ta sauya mata kamanni. Bayan ta kammala ba su labari, sai baki dayansu suka yi ta kukan murna, 'yarsu ta dawo. Daga nan sai aka raba wannan aure, domin mutum ba ya auren 'yar'uwansa.
Kurunkus.
Mun ciro wannan labarin daga littafin "Taskar Tatsuniyoyi" na Dakta Bukar Usman