ZAI ZAYEWAR KASA NA CIGABA DA RABA MU DA GIDAJEN MU A CIKIN BIRNIN KATSINA- MAZAUNA WASU UNGUWANNI
- Katsina City News
- 07 Jun, 2024
- 348
A cigaba da mika kokon barar da Mazauna Unguwannin Sabuwar Dutsin-Safe ,da malali da bayan gidan Taki a cikin brinin Katsina ke yi ga gwamnatin Jihar Katsina da ta sama musu mafita a wadannan unguwanni da wata babbar hanyar ruwa kebyi wa barazana.
Shugabannin wadannan al-ummomi Sun cigaba da jaddada irin matsalar da kalu-balen da rashin hanyar ruwa ke haifarwa a wannan yanki.
Mal. Abdulakdir Ango Saulawa ya bayyana cewa, wannan roko da Neman tallafin gwamanti ya zama wajibi, kasancewar wannan matsala tafi karfin wannan al'umma,koda yake ,yace sunyi iya aikin da zasu iya yi a matakin aikin gayya.
Ya bayyana cewa wannan Matsala ta rashin magudanan ruwa tajima shekara da shekaru tana ruguza musu gidaje da sauran matsaloli musamman a lokutan damina.
Mal. Ango Saulawa ya kara cewa suna da yakini da amannar cewa gwamnatin jiha Ta mal Dikko Radda tanada kunnuwan sauraren koken al-umma tareda share musu hawayen su, wannan daliline yasa suke kara roko da akawo musu dauki na gaggawa, musamman daminar bana datazo da karfi da iska.
Indai za'a iya tunawa wadannan al-ummomi sunyi koken rashin wadatattun hanyoyin ruwa na jaza musu asara ta dukiya da dama a kowace shekara, yayinda wasu daga ciki sukeyin kaura daga wadannan unguwanni domin tsira da rayuka da dukiyoyinsu.
Wannan dai ruwa yana fitowa ne daga titin Ring road ya biyo ta unguwannin Filin Sukuwa, Sabuwar low cost, da malali har ya zuwa Gadar Sani Danlami.