Gwamna Radda ya Ɗora Sanwar Shinfiɗa Kwalta daga Birchi Zuwa Wurma
- Katsina City News
- 04 Sep, 2023
- 1423
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Litinin Tawagar Injiniyoyi daga Hukumar Kula da Titunan jihar Katsina (KASAROMA) Bisa Jagoranci Shugaban ƙaramar hukumar Kurfi. Hon. Mannir Shehu, suka duba hanyar mai nisan kilomita 7 daga Birchi ta isa kauyen Sabon gari, Lambo, ta dangane da Wurma.
Injiniyoyin da suka duba wajen bisa sa'idon Babban Daraktan kula da Hanyoyi, Injiniya Abba Jamilu, sun tantance da kuma duba Yadi, tsawo da kuma gadojin da hanyar ta kumsa inda suka hada dukkanin bayanansu a rubuce zuwa ga Hukumar da ake saran ginin hanyar a karkashinta.
Da yake gabatar da jawabinsa a garin Wurma Hon Mannir Shehu ya bayyana tsawon zamunna da aka dauka ana so ayi wannan hanya, amma aAllah bai nufa ba. Inda yace tun zamanin tsohon Gwamnan jihar Kaduna kafin bawa jihar Katsina jiha, a lokacin Balarabe Musa, yazo har garin Wurma yace zaiyi hanya amma abin bai yiyu baba inda yayi Alƙawarin Asibiti da ita Hanyar da ake magana a yanzu. Amma Asibitin kawai aka yi, yace Lokacin Lawal Kaita ma, yaso yayi hanyar shima hakan bai yiyu ba, yace gwamnoni dai da dama hatta Aminu Bello Masari tsohon Gwamnan jihar Katsina shima yaso yayi hanyar amma bata samu ba, to amma munsan komai sai Allah ya nufa. Yace "Wannan Gwamnan na yanzu Dakta Dikko Umar Radda shiyama yazo garin nan, inda ya yi alƙawarin zai yi wannan hanya, gashi yau cikin kasa ga wata hudu ya turo Kwamitin Injiniyoyi domin dubawa da kai masa rahoto. Don haka muna da kyakkyawar fata akan Dakta Dikko Umar Radda.
Hon. Mannir ya kara da cewa, Wurma akwai kyakkyawan tsaro basu da wata matsala ta barayi ko 'yan Bindiga, yace ku sheda ne gashi kunzo kun gani kuma kun tabbatar. Don haka ya nemi da jama'ar garin Wurma da suyi ta Addu'a don neman karin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Tawagar ta samu rakiyar jami'an tsaro, 'yan Jarida da sauransu.