Majalisar Dokokin Katsina Ta Amince da Shugaban Riko na ƙaramar hukumar Dutsinma
- Katsina City News
- 05 Jun, 2024
- 363
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tantance gami da amincewa da Hon. Ibrahim Sada.
Majalisar ta amince da Hon. Ibrahim Sada a matsayin Shugaban Riko na karamar Hukumar Dutsinma.
Zaman Majalisar Dokokin Jihar Katsina na yau Laraba 6 ga watan Juni. An amince da Hon. Ibrahim Sada ne bayan gabatar da shi da Mataimakin Babban mai tsawatarwa na Majalisar, Hon. Salisu Hamza Rimaye, wanda ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda PhD, ya gabatar da shi.
Mambobin Majalisar sun tantance Ibrahim Sada ba tare da wata-wata ba, kasancewar karamar Hukumar Dutsinma na matukar bukatar jajirtaccen shugaba da zai bada gudunmuwa wajen kawar da matsalar tsaro a yankin.
Tantancewar Hon. Ibrahim Sada tazo cikin sauki bisa ga Kyakkyawar alaka dake tsakanin dan majalisar ta Dutsinma Hon. Abubakar Khamis da sauran membobin majalisar.
Kafin nan Ibrahim Sada Shine Shugaban hukumar Kula da Ayyukan Malaman Makarantu na jihar Katsina (Katsina State Teachers Service Board, T.S.B)