Dalilin Saurin Samun Karaya ga Tsaffi

top-news

Dalilin Saurin Samun Karaya Ga Tsofi 

Ƙashi, kamar sauran sassan jiki, ya ƙunshi rayayyun ƙwayoyin halitta. A kullum wasu ƙwayoyin halittar ƙashi suna mutuwa sannan a maye gurbinsu da sabbi. Haka rayuwar ke ci gaba!

A shekaru ƙasa da 30, lokaci ne da ƙasusuwa ke kaiwa ƙololuwar tsayi ko girma. Saboda haka, a wannan lokaci, yawan sabbin ƙwayoyin halittar ƙashi suna fin yawan ƙwayoyin halittar ƙashi masu mutuwa. Don haka, ƙashi zai ci gaba da tsayi da girma tare da kasancewa cikin ingantacciyar lafiya.

Sai dai, bayan shekaru 30, ƙwayoyin halittar ƙashi masu mutuwa suna fin sabbin ƙwayoyin halittar ƙashi yawa a kullum. Wannan dalili ne ke haifar da zaizayewar ƙashi yau da gobe.

Zaizayewar ƙashi na nufin raguwar nauyi, ƙwari da ingancin ƙashi. 

Domin haka, ƙashi zai zama marar ƙwari kuma marar nauyi. Wannan zai janyo barazanar saurin gamuwa da karayar ƙashi da zarar an samu tuntuɓe, faɗuwa ko bugu.

Amma bayan shekaru, akwai wasu ƙarin dalilan da suke janyo zaizayewar ƙashi kamar cutukan ƙashi, ƙarancin sinadaran kalsiyam, fatasiyam, bitamin D da sauransu. 

Bugu da ƙari, matan da suka daina jinin al'ada, galiban bayan shekaru 45 — 55, suna da ƙarin barazanar zaizayewar ƙashi da saurin samun karayar ƙashi.

© Physiotherapy Hausa