Gwamnan jihar Zamfara ya kara jaddada kudurinsa na kare rayukan al'ummar jihar
- Katsina City News
- 05 Jun, 2024
- 530
A faɗi-tashin da yake yi wajen samar da ingataccen tsaro, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Zamfara.
A ranar Talatar nan ne gwamnan ya halarci bikin yaye wasu dakaru na musamman, waɗanda ke ƙarƙarshin Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ake kira 'Agro Rangers' a Jihar Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, dakarun na 'Agro Rangers', jami'ai ne na musamman a Hukumar ta Sibil Difens, waɗanda suka samu horo mai zurfi.
Ya kuma ƙara da cewa, an horar da jami’an na musamman a shirye-shiryen gudanar da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ’yan bindiga a Jihar Zamfara.
A yayin jawabinsa a wajen bikin, gwamna Lawal ya yaba wa hukumar NSCDC bisa wannan shiri nasu. Ya ce, “Wannan ya zo ne a wani muhimmin lokaci kuma ya yi daidai da ƙudurinmu na ɗaukar ingantattun matakan yaƙi da rashin tsaro.
“Mun ɗauki wannan a matsayin babban mataki na tunkarar ƙalubalen da ya kawo cikas ga al'ummar mu wajen ayyukan noma, sana’o’in dogaro da kai, da sauran hanyoyin samar da abinci a jihar.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana harkokin tsaro da noma a matsayin muhimman abubuwan da suka sa a gaba. Mun ɓullo da matakai daban-daban don magance ƙalubalen tsaro da kuma bunƙasa noma a jihar. Don haka, muna kallon wannan shiri na jami’an Hukumar Sibil Difens a matsayin wani gagarumin mataki na ci gaba da ɗaukar matakan tsaro da muke ɗauka a matsayin gwamnati tare da jami’an tsaro da ke aiki a jihar.
“A matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da bada haɗin kai da cibiyoyi, ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane wajen yaƙi da duk wani nau’in miyagun laifuka. Mun himmatu wajen samar da tallafin da waɗannan cibiyoyi da ɗaiɗaikun mutane ke buƙata don gudanar da ayyukansu. Manufar farko ita ce tabbatar da tsaron al'ummominmu da kuma sanya su cikin aminci don ayyukan zamantakewa da tattalin arziki wanda zai sauƙaƙe ci gaban jihar da jama'a.
“Ina matuƙar fatan shirin hukumar NSCDC na samar da wani dakarun na musamman, wanda hakan zai samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, musamman waɗanda suka shafi harkar noma.
“Ina da alfahari da ƙaddamar da wannan dakaru. Ina yi muku fatan alheri bisa sauke nauyin da aka ɗora muku. Ina roƙon Allah Ya tsare ku, sannan Ya yi muku jagoranci."
Tun da farko, Kwamandan Rundunar Sibil Difens a Jihar Zamfara, Kwamanda Sani Mustapha, ya gode wa Gwamna Lawal da gwamnatin Jihar bisa tallafin da suka ba shirin horarwa da dakarun Agro Rangers.
“Yallabai, ɗimbin goyon bayan da ka ke baiwa rundunar ta sa muka kai ga haka. Muna godiya ƙwarai da gaske,” inji shi.
Kwamandan ya ƙara da cewa, Hukumar ta NSCDC ta himmatu wajen samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice a yankunan da ake fama da rikici.