Rigimar Sarautar Kano: Sanusi II Ya Samu Goyon Baya Daga Kungiyar Lauyoyin Najeriya
- Katsina City News
- 05 Jun, 2024
- 393
Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wani babban taro da ta gudanar a jihar A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, NBA ta amince da Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar Sarkin Kano Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama
A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar.
Wannan na zuwa bayan da shugabannin kananan hukumo 44 na Kano da hakiman su, kwamishinoni da wasu manyan jihar suka yi mubaya'a ga sabon sarkin.
Kungiyar NBA ta gayyaci Sanusi II taro
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar NBA ta amince da nadin Sarki Sanusi II ne bayan ta gayyace shi taronta na shekara da ke gudana yanzu a Kano.
La'akari da girman wannan taron, kungiyar lauyoyin ta gayyaci Sanusi Sarkin Kano na 16, domin ya gabatar da jawabin sanya albarka a matsayinsa na uban ƙasa.
An ce kungiyar ta NBA ba ta gayyaci Alhaji Aminu Ado Bayero ba, wanda dokar masarautar Kano ta 2024 ta kore shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 15.
Sarki Sanusi II ya yi magana kan shari'a
A ran Litinin ne babbar kotun tarayya da ke Kano ta shirya sauraron karar da aka shigar gabanta kan rigimar masarautar amma saboda yajin aikin NLC ba ta samu zama ba.
Sarki Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron kungiyar NBA ta bakin wakilinsa, Mahe Bashir Wali (Walin Kano) ya yi wa baki maraba da nuna girman al'adun jihar Kano. Sarkin ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama, wanda kuma ya ce bunkasar al'uma na tattare da karfin shari'a, in ji rahoton Independent.
Gwamnan Kano ya ƙalubalanci lauyoyi
A bangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kuwa, ya yi amfani da damar wajen ƙalubalantar NBA kan makomar umarnin kotuna biyu game da rigimar masarautar jihar. Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bappa Bichi ya nemi lauyoyin da suka rika wayar da kan abokan huldarsu kan hurumin kotuna a shari'a. Abba Yusuf ya ce akwai kotun da ba ta da hurumin sauraron shari'ar rigimar masarautar Kano kasancewar rigima ce ta cikin gida, wadda kotun jiha ke da hurumin saurare.
Sarki Sanusi II ne Sarkin Kano
-NBA Da yake zantawa da manema labarai kan rikicin masarautar Kano, Barista O.M Femi ya ce kungiyar NBA ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa. Barista O.M Femi ya ce: “Duk da haka, ba ka bukatar a gaya maka ko ka sanya tabarau kafin ka san cewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano na 16 a yanzu.
"Haka zalika, gayyatar Sarki Sanusi II zuwa wannan babban taron na NBA zai kara ba ka tabbaci na wanda muke kallo a matsayin Sarkin Kano na 16.