An fara gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a Zamfara
- Katsina City News
- 03 Jun, 2024
- 359
Yanzu haka dai an fara gudanar da wani muhimmin taro na masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya a jihar Zamfara.
Taron, wanda aka fara shi Litinin ɗin nan a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, ofishin kula da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifuffuka na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Nijeriya ne ya shirya shi.
Mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu Litinin ɗin nan a Gusau, ya bayyana cewa taron, wani shiri ne fayyacewa da lalubo hanyoyin mayar da martani game da matsalolin harkar tsaro da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Sulaiman Bala ya ƙara da cewa, wata tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙarƙashin jagorancin Oliver Stolpe, wanda kuma shi ne wakili a Nijeriya na UNODC, taron zai tattaro masu ruwa da tsaki, inda za su zauna na tsawon kwanaki uku.
Sanarwar ta ce, "A wani muhimmin abu na masu ruwa da tsaki, ofishin kula da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifuffuka na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNODC) ya shirya wani taron ƙara wa juna sani na kwana uku a kan harkar tsaro yau a Gusau.
“Taron ya samar da masu ruwa da tsaki na cikin gida, da wasu baƙi daga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda za su yi zuzzurfan nazari, samar da hanyoyin magance duk wani yanayi na tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar Zamfara.
"Taron ya bayyana ingantattun ayyuka da kuma hanyoyin da za a bi daga ciki da wajen Nijeriya wajen tunkarar waɗannan ƙalubale don samar da wani shiri na haɗin gwiwa."
A jawabinsa na buɗe taron, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, ƙwaƙƙwarar tawaga ta masana daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna aniyarsu ta haɗin gwiwa wajen magance ƙalubalen da ke addabar Zamfara, da suka haɗa da ’yan bindiga da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Ya ce, “Kwanan nan na ziyarci Majalisar Ɗinkin Duniya domin neman shiga tsakani don magance wasu matsalolin da muke fuskanta, inda na samu kyakkyawar alaƙa da Amina J. Mohammed, mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma sauran ɓangarorin da take jagoranta ciki har da shugaban ofishin kula da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.
"Saboda haka, wannan taron ƙara wa juna sani shaida ne na himmar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke da shi na cika alƙawuran da ta ɗauka don taimaka mana mu ƙara fahimtar yadda za mu magance ƙalubalen da mu ke fuskanta. Muna matuƙar godiya.
“Sama da shekaru goma, Zamfara tana fama da waɗannan matsalolin da ke kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar al’ummarmu da kuma kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Don haka gwamnatina ta ɗauki wannan ziyara da taron bita da muhimmanci, domin sakamakon zai nuna yadda manufofinmu za su kasance wajen dabarun yaƙi da waɗannan ƙalubale.
“Na yi farin cikin ganin cewa za a tattauna batutuwa da dama yayin taron.
“Waɗannan sun haɗa da bayyanar da tushen matsalolin rashin tsaro da aikata laifuka a jihar, kamar garkuwa da mutane, satar shanu, haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, da rikicin ƙabilanci, rawar da jami’an tsaro daban-daban na jihohi da cibiyoyin gargajiya suke takawa wajen yaƙar matsalolin, tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ga ƙarfafa shari'a a aikata laifuka.
“Hanyoyi da yanayin da ke haifar wa al’umma shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara da wanda za a bi wajen rigakafin shan muggan ƙwayoyi da sauran muhimman batutuwa, duk an shirya su don tattaunawa a wannan taro.
“Ina kira ga mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar kuma su bada himma don cin gajiyar ayyukan. Ya kamata ku saurara, ku koya, kuma ku bada gudunmawa mai inganci.
"A ƙarshe, ina fatan dukkanin mahalarta taron za su kasance masu amfanar al'umma. Kamar yadda na bayyana, shawarwarin da aka samar a nan za su kasance masu muhimmanci wajen tsara dabarunmu da ayyukanmu don magance matsalolin da mu ke fuskanta."