YAJIN AIKI: Kungiyar Kwadago ta rufe Ma'aikatun gwamnatin jihar Katsina
- Katsina City News
- 03 Jun, 2024
- 484
An wayi gari da yajin Aiki a fadin Najeriya, haka abin yake a jihar Katsina. Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Katsina ta bisa sahun takwarorin ta a fadin Nijeriya wajen garkame duk wasu ma'aikatun gwamnati.
Yajin aikin ya shafi ma'aikatun gwamnati Bankuna Asibitoci da kuma dai-dai kun wurare masu zaman kansu.
Ko dayake za'a iya cewa Yajin aikin kai tsaye bai shafi kasuwanci a birnin Katsina ba, amma masu hasashe na ganin cewa idan har yajin aikin ya dore zai iya taba kasuwanci, kuma yayi tasiri sosai.
A zagayen gani da ido, munga yanda al'umma ke ta hadahadar su, wasu yankunan ma kamar babu alamun yajin aikin. Wani da muka zanta dashi cewa "ya yaji da yajin aiki da ake a Nijeriya" sai yace, "Dama yau ana yajin aiki ne!" Duk da yana sana'ar Acaɓa amma ya bayyana mana cewa yanda ya saba haka ya gani a wajen kasuwancin sa.
Ko da dama yanayin zirga-zirga a Nijeriya ya karanta, kasantuwar tsadar manfetur amma zamu iya cewa al'amura sun ragu na zirga-zirgar jama'a kasantuwar kulle ma'aikatun gwamnati da wasu muhimman wurare.