Kwaɗayi ya cinye matasa ba su da tasiri a siyasar Najeriya'
- Katsina City News
- 03 Jun, 2024
- 478
Wani tsohon minista a gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ta 1999, ya soki matasan Najeriya saboda gazawarsu wajen tashi su ƙwatarwa kansu ƙwaƙƙwaran gurbi a harkokin siyasar ƙasar.
Alhaji Sani Zangon Daura ya ce ba a ga wani tasirin matasa a harkokin siyasar ƙasar ba, saboda akasari matasan sun zama masu kwaɗayi da rashin alƙibla, abin da ya sa wasu ke amfani da su kawai a matsayin karnukan farauta.
"Yanzu ba ka da wata jam'iyya ta samari. Duk wanda (ka ga) ya fito, kuɗi yake nema."
A cewar tsohon ministan noman zamanin gwamnatin Obasanjo, kamata ya yi matasa su kasance a kan gaba wajen kawo sauyi da ƙwatowa al'umma haƙƙi, amma ba haka lamarin yake ba a yanzu.
Ya bayyana damuwar cewa matasa sun zama lusarai ta yadda har "suna gani ana cutar su, ba sa iya komai".
Sani Zangon Daura na wannan jawabi a wani ɓangare na hirarrakin da BBC ta yi da ƙusoshin 'yan siyasa a kan cikar mulkin dimokraɗiyyar shekara 25 a Najeriya.
Ya dai ce a ganinsa, dimokraɗiyyar Najeriya ba ta samu wani ci gaban a-zo-a-gani ba, saboda har yanzu talaka ba shi da ƴancin zaɓar shugabannin da yake so su jagorance su.
Liberty tv