NAZIRI:ZAINAB ADO BAYERO (JUMMAI): HANNUN KA BA YA RUƁEWA KA YANKE KA YAR!
- Katsina City News
- 02 Jun, 2024
- 583
Ibrahim Sheme
Mutane da dama sun yi mamakin ganin guntun bidiyon da na wallafa a shafi na a daren jiya na tsakuren hirar da gidan talbijin na TVC ya yi da Zainab Ado Bayero, wadda ta gabatar da kan ta a matsayin ɗiyar marigayi Sarkin Kano. Da yawa sun yi mamakin jin cewa ita ɗiyar Sarkin ce, har suna shakka, ba domin komai ba sai saboda irin shigar ta wadda ta saɓa wa al'adar Hausawa. Wani ma cewa shi bai yarda 'yar Sarki Ado ba ce.
To, a gaskiya Zainab (Jummai) ɗiyar Takawa ce ta cikin sa. Mahaifiyar ta 'yar ƙabilar Edo ce daga Jihar Edo. Sarkin Auchi ne kakan ta. Uwar ta ce Sarkin Auchi ya ba Sarki Ado riƙo , wato ya kula masa da ita, lokacin da ta je karatu a Jami'ar Bayero, shi kuma Takawa ya aure ta, suka haifi 'ya'ya biyu, Zainab da ƙanen ta.
Zainab Jummai ta yi karatu a Ingila da nan Nijeriya. Yanzu mai shirya fim ce irin na tarihi da al'amuran yau da kullum, wato documentary.
Jummai ta zaɓi ta bi al'adar da ba ta Hausawa ba, musamman wajen shigar ta. Wannan zaɓin ta ne, kuma ba ka isa ka ce don ta yi shigar da ta saɓa da gidan su ita ba 'yar gidan ba ce. Uwa-uba, ta ce ita Musulma ce, kuma macen ƙwarai. Kuma ta yi kyakkyawar hulɗa da mahaifin ta.
Ba shakka, 'yan gidan ba su jin daɗin lamarin ta. A hirarrakin da ta yi da jaridu a baya, ta bayyana cewa sarakunan Kano da Bichi (wato waɗanda aka tuɓe kwanan nan) sun yi ƙoƙarin su hana ta yin fim ɗin da take shiryawa game da tarihin mahaifin ta da gudunmawar sa ga ƙasa. Dalilin su, a cewar ta, shi ne saboda ita mace ce kuma uwa-uba ba ta bin al'adar gidan su wajen suturta jiki. Ta ce shi ya sa duk wanda ta tunkara domin ya taimaka mata sai ya ƙi.
A cewar ta, duk da zagon ƙasa da ake yi mata kan wannan shirin fim, ba ta karaya ba domin mahaifiyar ta da wasu mutane daga kudu suna ba ta ƙarfin gwiwa.
To, Zainab dai 'yar Arewa ce ko mun ƙi ko mun so. Kuma 'yar gidan Dabo ce. Ko fuskar ta ka kalla ka san hakan ne. Saka ƙananan kaya da barin kai a buɗe ba su soke wannan cancantar ba. Ko ka ji wani ɗan gidan ya fito ya ƙaryata ta ne?
Abin da wasun mu ba su sani ba shi ne akwai 'ya'ya da yawa irin Zainab. Ni kai na na san su da ɗan yawa, wato 'ya'yan da waɗansu manyan Arewa (kai har ƙananan) suka haifa da wasu ƙabilu ko jinsi (misali Turawa ko Larabawa ko Canis) ko mabiya wasu addinan, kuma suka bi ɗabi'ar ɓangaren mahaifiyar su. Wani babba ɗin ma sai ya mutu sannan ake ganewa. Ana zaman makoki a gidan Bahaushe, sai a ga Bayarabiya ko wani Inyamiri sun zo a matsayin 'ya'yan mamacin. Sau da yawa, sai ka ga an hana su cin gado da ake rabawa - kamar yadda aka hana Zainab Ado Bayero.
Lokaci ya yi da ya kamata mu rage tsattsauran ra'ayi kan faruwar irin wannan al'amarin. Ba laifin 'ya'yan da aka haifa ba ne tunda ba su ne suka haifi kan su ba. Tilas mu rungume su a matsayin namu, domin ta haka ne za mu iya ɗora su kan hanyar da ta dace su bi. Kyara da tsana ko sharewa da kora ba su iya sauya lamarin su. Hausawa sun ce hannun ka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar!