Dan Majalisar Tarayya ya gabatar da koke kan Matsalolin tsaro a Jihar Katsina
- Katsina City News
- 31 May, 2024
- 528
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danja da Bakori, Honorabul Abdullahi Balarabe Dabai ya gabatar da kudurin koke a zauren majalisar tarayya kan matsalar tsaron da ta addabi jihar Katsina
Dan Majalisar a Katsina ya Bukaci Daukar Matakin Gaggawa Don Yaki da ‘Yan Bindiga da Tallafa wa Al’ummomin da hare-haren ya Shafa
Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, ya bukaci daukar mataki na gaggawa don magance yaɗuwar hare-haren ‘yan bindiga a Jihar Katsina.
A cikin wata takardar koke ta gaggawa da ya gabatar a zauren Majalisar Wakilai, Hon. Dabai ya jaddada bukatar gaggauta karfafa tsaro da tallafawa mazauna yankin da abin ya shafa.
Harin ‘yan bindiga na baya-bayan nan sun lalata yankin Bakori da Danja, wanda ya haifar da hasarar rayuka, Dukiyoyi, da kuma raba mutane da gidajensu. Al’umma na fama da matsalolin da suka biyo bayan hare-haren, ciki har da matsalolin rashin muhalli da na tattalin arziki.
Hare-hare na Kwanannan da tasirin su, sun shafi Unguwar Lamido, Guga, a karamar hukumar Bakori inda a ranar Asabar, 25 ga watan Mayu 2024, aka kai hari da yayi sanadiyar mutuwar Mutane takwas. Da hasarar awaki da shanu fiye da 100 da aka sace.
A takardar da Honorabul Abdullahi Balarabe ya karanto zauren Majalisar, ya kuma gabatar da ita ga shugaban majalisar ta kunshi cewa, "An kashe Mutane 26 a gidan Kare kusa da Lamido, iyakar Bakori da Faskari, a inda aka yi garkuwa da mata da ƙananan yara 32 da kwashe duk wasu kayan masarufi a yankin hadda takin zamani."
Haka zalika Gidan Tinjimi, a yankin Kakumi dake karamar hukumar Bakori an kashe mutum biyu da kone kaso mafi yawa daga gidajen garin." Inji shi.
Sauran wadanda Harin na 'yan bindiga ya shafa sun hada da Gidan Jaura, Kakumi, Sabon Layi duk a karamar hukumar ta Bakori.
Dangane da wadannan hare-hare, Hon. Dabai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su kara yawan jami’an tsaro a yankin Bakori da Danja don kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.
Haka kuma ya bukaci Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauran hukumomi su samar da tallafin gaggawa, ciki har da abinci, mafaka, da taimakon magunguna.
Ya kuma bukaci da a gudanar da bincike mai zurfi kan hare-haren don tabbatar da hukunta masu laifi da hana sake faruwar irin haka.
Dabai ya nemi a kaddamar da shirye-shiryen tallafa wa da sake maido da wadanda aka raba da muhallansu, ciki har da tallafi na musamman ga wadanda suka kamu da matsalolin tunani.
Kiran Hon. Dabai yana nuna bukatar gaggawa don daukar matakin dawo da zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina, da tabbatar da jin dadin mazauna yankin tare da kwanciyar hankalin al’umma.