GWAMNATIN ZAMFARA DA MANYAN AYYUKA A CIKIN SHEKARA ƊAYA
- Katsina City News
- 30 May, 2024
- 306
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa ayyukan samar wa al'umma mafita da gwamnatinsa ke yi na samun tagomashi sosai, kuma an samu gagarumin sakamako cikin shekara guda.
Gwamnan ya ƙaddamar da manyan ayyuka a Ƙananan Hukumomi takwas, wanda aka fara a Ƙaramar Hukumar Gummi a ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a Gusau ranar Alhamis ɗin nan, ya bayyana cewa an ƙaddamar da wasu ayyuka huɗu a babban birnin jihar, Gusau da Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
A sanarwar ta ce, gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da ɗaya daga cikin ayyukan tituna a Gusau: gyaran sakatariyar J.B. Yakubu ta jihar da kuma makarantar Tsangaya ta zamani da ke Ƙananan Hukumomin Gusau da Ƙauran Namoda.
“A ranar Talata, 28 ga watan Mayu, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da babbar hanyar da ta haɗa shataletalen UBA zuwa Freedom Square da ke ƙwaryar garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
“Hanyar wani ɓangare ne na aikin sabunta biranen da gwamnatin ke ci gaba da yi, kuma Ambasada Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ne ya ƙaddamar da shi.
A ranar Talata, 28 ga watan Mayu ne Gwamna Lawal ya ƙaddamar da Makarantar Tsangaya ta zamani a Ƙauran Namoda.
“Makarantar Tsangaya da ke Kauran Namoda ce za ta ɗauki nauyin kula da yankin Zamfara ta Arewa, bayan kwana biyu da ƙaddamar da wata a Gummi, da nufin yi wa al’ummar mazaɓar Zamfara ta Yamma hidima. Makarantar Tsangaya ta uku kuma tana Gusau ne a gundumomin Zamfara ta tsakiya.”
A jiya, 29 ga watan Mayu, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wani muhimmin aiki, ginin Sakatariyar J. B. Yakubu, wadda ita ce babbar sakatariyar gwamnatin jihar Zamfara.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin ranar 29 ga watan Mayu, Gwamna Lawal ya jaddada cewa a cikin watanni 12 da suka gabata gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai. “Mun hada ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran laifuka, mun yi gyara a sassa masu muhimmanci na ilimi, kiwon lafiya, da noma, mun ƙaddamar da ayyukan sabunta birane, da gyara tsarin ma’aikatun gwamnati, da inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a jihar, da kuma samar da ingantaccen tsarin gudanarwa a ma’aikatun gwamnati”.
A lokacin da yake ƙaddamar da Makarantar Tsangaya ta zamani da ke Gusau, Gwamna Lawal ya ƙara jaddada cewa, makarantun Tsangaya da aka sabunta, an tsara ta ne domin haɗa abubuwan da suka shafi ilimin zamani na Boko da koyarwar addinin Musulunci a lokaci guda.
“Kamar yadda na ambata a Gummi da Ƙaura Namoda, tsarin karatun Tsangaya ta kasance wani ɓangare na al’adunmu shekaru aru-aru. Ta kasance tushen ilimi da tarbiyya a cikin al'ummomin Musulmi a arewacin Nijeriya. Kusan kowane yaro ɗan Musulmi da ya girma a wannan yanki ya sami irin wannan nau'in ilimi.
“Wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ƙalubalen da jihar Zamfara ta samu matsayi mafi girma. Ta hanyar buɗe wa waɗannan yara sabbin damarmaki, muna fatan za mu zaburarwa da yawa daga cikinsu da ƙwarin gwiwar ci gaba da neman ilimi a nan gaba, ta yadda za su inganta rayuwarsu da kuma bayar da gudunmawar ci gaban jiharmu.”