Taron karawa juna sani da Gwamnatin jihar Katsina haɗingwiwa da Kamfanin Matsa Media Links suka shirya
- Katsina City News
- 27 May, 2024
- 443
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Litinin 27 ga watan Mayu 2024 Kamfanin Matasa Media Links masu jaridar Katsina Times da Taskar Labarai hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Katsina suka shirya wani taro na Karawa Juna sani ga ma'aikatan gwamnatin jihar Katsina akan yanda zasu inganta Ayyukan su.
Taron da aka gayyato Masana daga jami'o'i daban-daban sun fara gabatar da kasidar su a ranar farko.
Babban Bako da ya fara gabatar da kasidar shine tsohon shugaban Ma'aikatan jihar Katsina Alh. Idris Tune, wanda ya gabatar da Kasida da a turance akai wa take da "Freedom of Speech and oath of secrecy in information management."
Sai kasida ta biyu daga Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi daga jami'ar Bayero dake Kano, inda ya gabatar da Kasidar sa mai taken "New Media Documents leakages and digitalizing Office; what Staff of Katsina state Government should do ".
Shugaban Makarantar Katsina state Institute of Technology and Management studies, Dakta Babangida Abubakar Albaba ne zai gabatar da tasa Kasidar mai taken "How digitalized office work would reduce documents leakages."
Zamu kawo maku yanda taron zai kasance a ranar Talata.