Jami'ar Umaru Musa Yar'adua ta Karrama Tsohon Gwamna Aminu Bello Masari da Digiri na Girma
- Katsina City News
- 26 May, 2024
- 287
A ranar Asabar, 25 ga Mayu, 2024, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, tare da digirin girmamawa na digiri na uku a fannin kimiyyar siyasa.
A yayin bikin yaye daliban, wanda aka hada taron karo na 9 zuwa na 13, jami’ar ta karrama wasu fitattun mutane da dama bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar musamman a fannin ilimi.
Daga cikin wadanda aka karrama akwai tsohon gwamnan farar hula na farko a jihar Katsina, Alhaji Saidu Barda; Marigayiya Hajiya Hassu Iro Inko; Alhaji Garba Ammani Funtua, (wanda wani dan uwansu ya karbi lambar yabon a madadin su) da Alhaji Tijjani Dan Dutse.
A wani lamari makamancin haka, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranci rantsar da Sanata Ibrahim Ida (Wazirin Katsina) a matsayin sabon shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’adua, karo na biyu (Chancellor) haka zalika Sanata Ibrahim Ida ya jagoranci baiwa Rt. Hon. Aminu Bello Masari da sauran wanda jami'ar ta zaba, mika masu lambar girmamawar.
Bikin ya samu halartar manyan baki da dama da suka hada da mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruq Lawal Jobe; Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Sani Ali JB, tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina, Qs. Mannir Yakubu, Mai shari’a Amiru Sanusi, Alhaji Kabir Mashi, da tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal.
Wakilan majalisar zartaswa ta jihar Katsina, ‘yan majalisar dokokin jihar, tsofaffin jami’an gwamnati, wakilan Sarkin Katsina da Daura, da ‘yan uwa, abokan arziki, da sauran masu hannu da shuni, sun halarci taron.