HUKUMAR HISBAH A MAKON DA YA GABATA
- Katsina City News
- 25 May, 2024
- 489
Wasu Muhimman Al'amurra da Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Aiwatar bisa Jagorancin shugaban nata Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) daga 19 ga watan Mayu zuwa 24 ga watan na Mayu.
Bisa Dokokin da aka kafa hukumar, an kafa ta ne don kawo Ɗa'a, Tarbiyya, da Kawar da ko wace irin Ɓarna (Rashin Da'a) a jihar Katsina tare da sasanta matsalolin cikin gida musamman Ma'aurata da makamantansu su.
Hukumar ta ci-gaba da kai samame a gidajen sheƙe Aya (Gidan Kashe Ahu) da nufin tsaida barna da ta sabawa Shari'a ta Addini musulunci da Al'adun jihar Katsina.
Hakan ya bayyana Nasarar Hukumar inda ta kamo mata masu zaman kansu, a cikin Makon fiye da 50 a wurare daban-daban tare da tantance garuruwan da suke, ko Unguwannin su. Neman Iyayen su dangi ko 'Yan uwa, tare da gabatar da Nasiha akan su kansu Matan masu zaman kansu.
Wasun su, hukumar ta Hisbah ta maidasu makarantar Islamiyya bisa sharadi da tabbatar da Nadamarsu da Al'kawarintar dasu akan zasu cigaba a rayuwa kamar sauran mutanen kirki har Allah ya kawo masu mazajen Aure.
Wasu kuma an tsare su tare da karantar da su da maido dasu hayyacin su, kasantuwar nisa da sukai akan Ayyukan su na Badala.
Haka kuma Hukumar bisa jagorancin Dakta Abu Ammar ta shiga tsakani Don Daidaita Ma'aurata da suka samu Matsala ta rabuwar Aure, inda shugaban hukumar ya bibiyi lamarinsu wadanda keda matsalar rashin fahimta, akan Ilimi Auren aka fadakar da su, wadanda kuma halin rayuwa ta yau da kullum ne ya haddasa rabuwa, Malam Abu Ammar ya dauki wani dawainiya tare da bada gudunmawa (Tallafi) don maida Auren.
Haka kuma duk a cikin Makon 19 zuwa 24 ga watan hukumar ta kai samame a unguwar kofar guga tayi Nasarar kama wasu matasa masu satar wayoyin wutar lantarki da karafuna da gwamnati ta kafa don amfanin al'umma.
Hukumar ta cigaba da zaman sasanci a ko wane lokaci don ganin an maido da tsari doka da oda a fadin jihar Katsina, haka zalika hukumar tana kara kira da jan hankali ga Matasa Maza da Mata, da su kaucewa duk wani abu da zai sa su shiga hannun ta, tana kira garesu da su zama jakadu na gari da za'ai alfahari dasu. Haka kuma iyayen yara su sanya ido akan 'ya'yan su, su bawa hukumar Hisbah goyon baya akan dakile ko wace irin barna don samun gobe mai kyau, a gudu tare a tsira tare.
Katsina State Hisbah Board
Asabar 25/05/2024